An damke buhuhunan garin Kwaki cike da ganyen 'Wiwi' (Hotuna)

An damke buhuhunan garin Kwaki cike da ganyen 'Wiwi' (Hotuna)

Jami'an hukumar hana fataucin muggan kwayoyi watau NDLEA a jihar Edo sun bankado yadda akayi kokarin fitar da kilon tabar Wiwi 83 boye cikin buhuhunan garin kwaki daga jihar.

Yan fasa kwabrin sun yi kokarin haka ne duk da dokar hana sufuri tsakanin jihohi a Najeriya sakamakon cutar Coronavirus.

An damke buhuhunan tabar Wiwin ne a cikin tashar manyan Motoci aka fi sani da Aviele trailer park, dake karamar hukumar Etsako ta yammacin cikin Edo.

Kwamandan hukumar NDLEA a jihar, Buba Wakawa, wanda ya sanar da wannan nasara a Benin City, ya jinjinawa jami'an yankin Auchi kan namijin kokarin.

A cewarsa, "hafsoshin yankin Auchi sun kai farmaki shararren tashar Tirela ne sakamakon rahoton leken asiri da suka samu cewa an boye bushasshen ganyen wiwi takwas (8) cikin buhuhunan garin kwaki da ake kokarin fitar dasu daga jihar."

"Wannan babban nasara ne kuma ina yabawa hafsosohin bisa kwarewarsu da jajircewansu."

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

An damke buhuhunan garin Kwaki cike da ganyen 'Wiwi' (Hotuna)
Buhun gari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Asibitin ABUTH Shika ta fara cika da masu cutar Korona - Masarautar Zazzau ta koka

An damke buhuhunan garin Kwaki cike da ganyen 'Wiwi' (Hotuna)
Buhun wiwi
Asali: Twitter

A wani harin da suka kai dajin Uzebba, hukumar ta damke kilo 20 na kwayar wiwi da kilo 13 ganyen.

Kwamandan ya gargadi masu safarar muggan kwayoyi su ajiye wannanhali ko s shirya fuskantar fushin hukuma.

"Gano kwayoyi da wuri duk da yadda ake kokarin boyesu babbar alama ce dake nuna cewa dillalan Wiwi ba zasu tsira daga bincikenmu ba."

"Muna nan a shirye domin yakar safarar muggan kwayoyi." Kwamandan ya ce.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel