'Yan jami'yyar APC 10,000 sun koma PDP a Kwara

'Yan jami'yyar APC 10,000 sun koma PDP a Kwara

Dubban 'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kwara a ranar Alhamis sun sauya sheka sun koma jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Wadanda suka sauya shekan sun fito ne daga mazabar Kwara ta Arewa kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Tsaffin yan jamiyyar na APC a baya bayan nan sun nuna rashin jin dadinsu da yadda rikici ya yi yawa a jamiyyar tun bayan da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya karbi mulki.

Wadanda suka hallarci taron wakilai ne da aka zabo daga kananan hukumomi biyar da ke karkashin mazabar ta Kwara ta Arewa don biyaya ga sharrudan dakile yaduwar korona a cewar shugabansu Hon. Manzuma Kawu Dogo.

'Yan jami'yyar APC 10,000 sun koma PDP a Kwara
'Yan jami'yyar APC 10,000 sun koma PDP a Kwara
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya yi ikirarin cewa, "mun kai kimanin 10,000 daga gundumu 58 da ke mazabar."

Dogo ya ce sun fice daga APC ne saboda rikicin da ke tsakanin shugabanin jamiyyar da mambobi da aka ce rashin bin kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya janyo hakan.

Ya ce an tauye wa yan jamiyya hakokinsu kuma ana musguna tare da cewa an gaza cika alkawurran da aka dauka yayin yakin neman zabe.

"shugabanin sun gaza tafiyar harkokin jamiyyar saboda rashin adalci da rashin tafiya tare da sauran mambobin jam'iyyar," in ji shi.

Ya ce zaben kananan hukumomi da za a yi a nan gaba zai fara korar jamiyyar APC mai mulki daga jihar.

Bayan jira da muka yi na shekara daya, mun gano gaskiya wadda hakan yasa dole muka fice daga jam'iyyar don tsare mutuncin mu.

Dogo ya yi karin bayani cewa "Burin mu shine kawo canji mai amfani da alummar mu. Kamar yadda kowa ke iya gani babu wani abu da PDP za ta iya bamu yanzu. Ficewar mu daga APC zuwa PDP ba don neman abin duniya bane."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel