Asibitin ABUTH Shika ta fara cika da masu cutar Korona - Masarautar Zazzau ta koka

Asibitin ABUTH Shika ta fara cika da masu cutar Korona - Masarautar Zazzau ta koka

Masarautar Zazzau a jihar Kaduna ta koka kan tashin gwauron zabo da adadin masu cutar Coronavirus ke yi a cibiyar kulawar da ke asibitin koyarwan jami'ar ABU, Shika Zaria.

Yayinda yake magana a wata ganawar wayar da kai a Zariya. Salanken Zazzau kuma shugaban kiwon lafiyar masarauta, AbdulKadir Salanke, ya ce cibiyar ta fara cika saboda karuwar masu cutar da ake samu a Masarautar.

A cewarsa, mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris. ya gayyaci dakatai ne da shugabannin addini zaman wayar da kan ne saboda sun fi kusa da a'l'umma kuma zasu taimaka wajen yada sakon.

Ya yi kira ga jama'ar Zazzau su bi umurnin hukumomin kiwon lafiya domin takaita yaduwar cutar saboda gaskiya ce kuma tana daukan rayuka.

Salanke ya mike godiyar masarautar ga gwamnati bisa hadin kai wajen samar da cibiyar killace masu cutar COVID-19 mai daukan mutane 20 a ABUTH.

TSOKACI:

A bangaren gwamnati kuwa, mataimakin diraktan hukumar cigaban kananan asibitoci, Hamza Ikara ya ce cutar COVID-19 ta yadu a kananan hukumomin jihar guda tara yanzu.

Sun hada da Igabi, Chukun, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta kudu, Zaria da Sabon Gari, Soba, Giwa da Makarfi.

Ikara ya ce an zabi gudanar da taron a Zariya ne saboda itace hedkwatar masarautar Zazzau wacce ta kunshi kananan hukumomi 8 cikin 9 da aka ambata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel