Majalisa za ta kwace wa IGP ikon nada kwamishinonin 'Yan sanda

Majalisa za ta kwace wa IGP ikon nada kwamishinonin 'Yan sanda

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta fara daukan matakai domin kwace wa Sufeta Janar na Rundunar 'Yan sanda (IGP) ikon nada kwamishinonin yan sanda da canja musu wurin aiki.

Ta mayar da wannan ikon zuwa ga Hukumar Kula da Al'amuran 'Yan sanda (PSC), wacce za ta tabbatar anyi wannan nadin bisa tsarin daidaito tsakanin jihohin Najeriya.

Majalisar ta kuma bawa kwamitin daukan sabbin yan sanda karkashin jagorancin Sufeta Janar na Yan sanda ikon daukan sabbin jami'ai.

Majalisa za ta kwace wa IGP ikon nada kwamishinoni
Majalisa za ta kwace wa IGP ikon nada kwamishinoni. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ta kuma wajabta wa IGP mika wa ofishin Attoney Janar na kasa ,AGF, rahoton kamen da hukumar yan sandan ta yi duk bayan watanni hudu yayin da kwamishinonin yan sanda za su mika makamancin irin rahoton ga Attoney Janar na jihohinsu.

Wannan na cikin sabon dokar da Majalisar ta yi bayan yin kwaskwarima ga dokar 'yan sanda don tabbatar da cewa an kula da hakkokin yan adam.

Sashi na 21 na sabon dokar yan sandan da majalisar ta amince da shi ya daura wa IGP nauyin daukan sabbin yan sanda da jamia'i ta kafa kwamitin kula da daukan sabbin 'yan sandan wacce za ta zartar da hukunci na karshe.

Sashi na 28 na sabon dokar ya ce bai halasta 'yan sanda su kama wani mutum daban ba a madadin wanda ake zargi da aikata laifi.

Har wa yau, sashi na 29 ya bayyana cewa bai halasta a ci zarafi ko keta hakkin wanda aka tafi kama wa ba domin yana da daraja da kima a matsayinsa na dan adam.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel