Zaben Edo da Ondo: Babu wanda zai jefa ƙuri'a idan ba shi da takunkumin rufe fuska - INEC

Zaben Edo da Ondo: Babu wanda zai jefa ƙuri'a idan ba shi da takunkumin rufe fuska - INEC

- Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta tsara wasu sigogi da za a yi amfani da su yayin gudanar da zabukan gwamnonin jihar Ondo da Edo.

- INEC ta tsara wasu ka’idoji na kada ƙuri'a yayin zaben gwamnoni na Edo da Ondo

- Hukumar zaben ta sanya takunkumin rufe fuska ya zama tilas ga masu kada ƙuri'a

- Ta kuma bayyana karara cewa ba za a yi amfani da duk wani tukunkumin rufe fuska ba mai dauke da tambarin kowace jam'iya ta siyasa

Hukumar Zabe Ta Kasa Mai Zaman Kanta INEC, ta shata wasu sharuɗa da za a yi amfani da su yayin gudanar da zaben gwamna a jihohin Ondo da Edo da ke tafe.

INEC ta gindaya wannan ka'idodi yayin zaman nesa-nesa da juna na farko da aka yi ta hanyar bidiyo da aka hada da intanet, wanda ta gudanar a ranar Laraba, 3 ga watan Yuni.

Shugaban Hukumar na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu, shi ne ya jagoranci zaman wanda aka fidda sigogin da za a yi amfani da su yayin gudanar da zabukan a jihohin biyu.

Shugaban Hukumar INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu
Shugaban Hukumar INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu
Asali: Twitter

Da yake jawabi a yayin taron, kwamishinan INEC na kasa, Okechukwu Ibeanu, ya bayyana karara cewa, sanya takunkumin rufe fuska ya zama tilas ga masu kada ƙuri'a yayin zabukan.

Ibeanu ya ce duk wanda yaki sanya takunkumin rufe fuska ko kuma aka kama ba tare da takunkunmin rufe fuskar ba za a nemi ya bar wurin cikin salama.

Doriya a kan hakan, kwamishinan Hukumar ya ce ba a bukatar a yi amfani da tukunkumin rufe fuska mai dauke da tambarin kowace jam'iya ta siyasa ba.

KARANTA KUMA: Babu wata kofa ta samun kudin shiga da cutar korona ba ta yi wa illa ba - Lai Mohammed

Haka kuma ya ce, a wannan lokaci, Hukumar zaben ba za ta dauki nauyin tanadar takunkumin rufe fuska ba ga masu kada ƙuri'a.

A bangare daya kuma, Legit.ng ta ruwaito shugaban Hukumar zaben yana cewa, annobar korona ba za ta hana gudanar da zabe ba ko ina a fadin kasar nan.

Shugaban Hukumar ya ce jingine zabe a Najeriya sanadiyar cutar korona zai iya kasancewa cikas ga tsari na dimokuradiya.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel