Da alamun wasu sabbin kudade $3.3 billion sun yi batar dabo hannun CBN - Majalisar dattawa

Da alamun wasu sabbin kudade $3.3 billion sun yi batar dabo hannun CBN - Majalisar dattawa

Kwamitin majalisar dattawa kan baitul mali, a ranar Laraba, ta tuhumci babbar bankin Najeriya CBN kan wani kudi $3.3 billion (Kimanin N1.2 trillion da ake zargin sun bi iska, The Cable ta ruwaito.

An nemi kudin an rasa ne daga cikin kudi $21.3 billion da kamfanin karbar haraji FIRS ta baiwa CBN na harajin kasashen waje na shekarar 2015 .

Ofishin mai bin diddigin tarayya ya aikewa majalisa wasikar bukatar bincike kan kudin.

Mai bin diddigin watau Odito-janar ya bayyana cewa yayinda hukumar FIRS ta alanta cewa an samu $21.3 billion matsayin kudin harajin kasashen waje a 2015, $18 billion bankin CBN ta rubuta an samu.

Amma wakilin bankin, wanda shine mataimakin gwamnan bankin, Edward Adamu, ya yi bayanin cewa an samu banbanci ne a kudin saboda canjin da aka samu a farashin dala($).

Yace: "Ba bacewa $3.3 billion sukayi ba kuma ba wai anki bayyanawa bane, an samu banbanci ne saboda canjin da aka samu a kasuwar canjin dala a lokacin."

Amma kwamitin tayi watsi da bayaninsa.

TAMBIHI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Da alamun wasu sabbin kudade $3.3 billion sun yi batar dabo hannun CBN - Majalisar dattawa
Hoto: CBN
Asali: UGC

Shugaban kwamitin, Sanata Matthew Urhoghide, ya bukaci bankin CBN ta sake bayyana gaban kwamitin ranar Litinin da takardun hujja dake nuna cewa canjin farashin dala ne ya janyo hakan.

Bayan zaman, Sanata Urughide ya bayyanawa manema labarai cewa: "Yayinda rahoton FIRS ya nuna cewa an samu$21.3 billion, rahoton CBN na nuna $18 billion.”

"Yayinda muka tambayi CBN dalilin da yasa aka samu banbanci, babbar bankin ta yi ikirarin cewa canjin farashin dalane, sai muka umurci wakilan bankin su kawo mana hujjojin hakan."

"Akwai tuhume-tuhume 13 da aka kawo mana kan CBN. Sun yi bayani kan wasu yayinda ba suyi gamsasshen bayanai kan wasu ba, musamman na $3.3 billion."

A bangare guda, an sammaci hukumar sojin Najeriya, hukumar yan sanda, da hukumar EFCC kan rashin bayanin kudaden da suka kashe na shekaru da yawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel