Jihohi 36 da aka samu bullar cutar korona a Najeriya - NCDC

Jihohi 36 da aka samu bullar cutar korona a Najeriya - NCDC

- A yanzu cutar korona ta bulla a jihohi 35 na Najeriya da kuma babban birnin kasar na Tarayya

- Jihar Legas ce ke jan ragama inda ta harbi mutum 5,440

- Jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba cikin dukkanin jihohin Najeriya

- A halin yanzu cutar ta harbi mutum 11,666 sai kuma mutum 3,329 da suka samu waraka, yayin da mutum 315 suka riga mu gidan gaskiya

Watanni uku bayan bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 35 na kasar da babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Laraba, 3 ga watan Yuni.

Legit.ng Hausa ta kawo muku jerin jihohin da ta bulla, adadin wadanda suka kamu, adadin wadanda suka samu waraka, adadin wadanda ke asibiti yanzu, adadin wadanda suka mutu.

Lagos: Adadin kamuwa 5,440, Wadanda ke asibiti 4,495 , Wadanda suka warke 878, Mutuwa 67

Kano: Adadin kamuwa 970, Wadanda ke asibiti 607 , Wadanda suka warke 318, Mutuwa 45

Abuja: Adadin kamuwa 763, Wadanda ke asibiti 538 , Wadanda suka warke 205, Mutuwa 20

Katsina: Adadin kamuwa 371, Wadanda ke asibiti 244 , Wadanda suka warke 108, Mutuwa 19

Edo: Adadin kamuwa 341, Wadanda ke asibiti 250 , Wadanda suka warke 77, Mutuwa 14

Oyo: Adadin kamuwa 317, Wadanda ke asibiti 212 , Wadanda suka warke 98, Mutuwa 7

Kaduna: Adadin kamuwa 297, Wadanda ke asibiti 114 , Wadanda suka warke 175, Mutuwa 8

Borno: Adadin kamuwa 296, Wadanda ke asibiti 95 , Wadanda suka warke 175, Mutuwa 26

Ogun: Adadin kamuwa 282, Wadanda ke asibiti 113 , Wadanda suka warke 160, Mutuwa 9

Jigawa: Adadin kamuwa 274, Wadanda ke asibiti 129 , Wadanda suka warke 140, Mutuwa 5

Rivers: Adadin kamuwa 269, Wadanda ke asibiti 177 , Wadanda suka warke 76, Mutuwa 16

TAMBIHI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Bauchi: Adadin kamuwa 246, Wadanda ke asibiti 16 , Wadanda suka warke 222, Mutuwa 8

Gombe: Adadin kamuwa 169, Wadanda ke asibiti 38 , Wadanda suka warke 124, Mutuwa 7

Sokoto: Adadin kamuwa 115, Wadanda ke asibiti 4 , Wadanda suka warke 97, Mutuwa 14

Kwara: Adadin kamuwa 111, Wadanda ke asibiti 73 , Wadanda suka warke 37, Mutuwa 1

Plateau: Adadin kamuwa 109, Wadanda ke asibiti 25 , Wadanda suka warke 82, Mutuwa 2

Delta: Adadin kamuwa 106, Wadanda ke asibiti 71 , Wadanda suka warke 27, Mutuwa 8

Nasarawa: Adadin kamuwa 88, Wadanda ke asibiti 66 , Wadanda suka warke 19, Mutuwa 3

Zamfara: Adadin kamuwa 76, Wadanda ke asibiti 0 , Wadanda suka warke 71, Mutuwa 5

Ebonyi: Adadin kamuwa 63, Wadanda ke asibiti 55 , Wadanda suka warke 8, Mutuwa 0

Yobe: Adadin kamuwa 52, Wadanda ke asibiti 21 , Wadanda suka warke 24, Mutuwa 7

Osun: Adadin kamuwa 47, Wadanda ke asibiti 8 , Wadanda suka warke 35, Mutuwa 4

A/Ibom: Adadin kamuwa 45, Wadanda ke asibiti 29 , Wadanda suka warke 14, Mutuwa 2

Adamawa: Adadin kamuwa 42, Wadanda ke asibiti 11 , Wadanda suka warke 27, Mutuwa 4

Neja: Adadin kamuwa 41, Wadanda ke asibiti 31 , Wadanda suka warke 9, Mutuwa 1

Imo: Adadin kamuwa 39, Wadanda ke asibiti 25 , Wadanda suka warke 14, Mutuwa 0

Kebbi: Adadin kamuwa 33, Wadanda ke asibiti 0 , Wadanda suka warke 29, Mutuwa 4

Ondo: Adadin kamuwa 33, Wadanda ke asibiti 8 , Wadanda suka warke 21, Mutuwa 4

Ekiti: Adadin kamuwa 25, Wadanda ke asibiti 5 , Wadanda suka warke 18, Mutuwa 2

Enugu: Adadin kamuwa 24, Wadanda ke asibiti 12 , Wadanda suka warke 12, Mutuwa 0

Bayelsa: Adadin kamuwa 21, Wadanda ke asibiti 11 , Wadanda suka warke 8, Mutuwa 2

Taraba: Adadin kamuwa 18, Wadanda ke asibiti 8 , Wadanda suka warke 10, Mutuwa 0

Abia: Adadin kamuwa 15, Wadanda ke asibiti 8 , Wadanda suka warke 7, Mutuwa 0

Benue: Adadin kamuwa 13, Wadanda ke asibiti 12 , Wadanda suka warke 1, Mutuwa 0

Anambra: Adadin kamuwa 12, Wadanda ke asibiti 8 , Wadanda suka warke 3, Mutuwa 0

Kogi: Adadin kamuwa 3, Wadanda ke asibiti 3, Wadanda suka warke 0, Mutuwa 0

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel