Yadda matashi mai shekara 21 ya kashe abokinsa saboda budurwa a Bauchi

Yadda matashi mai shekara 21 ya kashe abokinsa saboda budurwa a Bauchi

'Yan sanda sun kama wani matashi, Ishaku mai shekaru 21 da haihuwa saboda kashe abokinsa, Zeloti ta hanyar daba masa wuka don rikici a kan budurwa.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani mashaya a garin Dass a ranar Juma'a 29 ga watan Mayu inda Ishaku ya caka wa Zeloti wuka har sau uku kan musun da suke yi a kan wanene ainihin saurayin yarinyar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakili ya tabbatar da afkuwar lamarin kamar yadda LIB ta ruwaito.

Yadda matashi mai shekara 21 ya kashe abokinsa saboda budurwa a Bauchi
Yadda matashi mai shekara 21 ya kashe abokinsa saboda budurwa a Bauchi. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: 'Yan kungiyar Barcelona 5 sun kamu da korona

Wakili ya ce an garzaya da Zeloti John zuwa babban asibitin garin Dass inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

An birne shi a ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2020.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya ce an kama wanda ake zargin kuma yana tsare yayinda ake cigaba da binciken gano musababbin mutuwar mammacin.

A wani rahoton, mun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Baba Tela ya kamu da cutar COVID-19 wadda aka fi sani da korona.

Babban mai taimakawa gwamnan Bauchi a fanin watsa labarai, Mukhtar Gidado ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a Bauchi a ranar Laraba.

Ya ce an tabbatar da hakan ne bayan gwajin da Hukumar NCDC ta yi masa sakamakon alamomin cutar da suka bayyana a jikinsa.

Mr Gidado wanda shine shugaban kwamitin yaki da Korona da Zazzabin Lassa tuni ya killace kansa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ya ce, "Ana sanar da alumma cewa mai girma Sanata Baba Tela, mataimakin gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kwamitin yaki da COVID-19 ya kamu da coronavirus.

"Ya kamu da cutar ne a lokacin da ya ke gudanar da aikinsa na jagorancin kwamitin yaki da cutar.

"Saboda haka, mai girma, Baba Tela ya killace kansa a Bauchi kuma kwararrun maaikatan lafiya suna bashi kulawa."

Hadimin gwamnan ya ce Hukumar NCDC ta dauki samfuri daga dukkan hadimansa na kusa da suke hulda kuma an bukaci su killace kansu yayin da suke dakon sakamakon gwajin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel