Hotunan yadda titunan Kano suka cika da mutane bayan sassauta dokar kulle

Hotunan yadda titunan Kano suka cika da mutane bayan sassauta dokar kulle

Duk da sassauta dokar kulle da gwamnatin tarayya ta yi, gwamnatin Jihar Kano ta ce har yanzu dokar kulle tana aiki a jihar a ranakun Litinin, Talata, Alhamis da Asabar.

Ta kuma fitar da sabbin kaidoji da dokoki kan yadda za a rika zuwa kasuwanni da wasu wuraren hada-hadan mutane a jihar don rage yiwuwar yada cutar korona.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanarwar ta ce bayan tuntubar kwararru a bangaren lafiya da bita kan halin da ake ciki a Kano, an bayar da izinin zirga-zirga da bude wuraren bauta a ranakun Lahadi, Laraba da Juma'a daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.

DUBA WANNAN: Kotu ta tsare mutumin da ya yi zina da surukarsa

Kasancewar yau 3 ga watan Yuni ya fada a ranar Laraba, Kanawa sun fita kwansu da kwarkwata domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Hotunan da suka fito daga jihar ta Kano ya nuna mafi yawancin mutane ba su kiyaye dokar bayar da tazara ko rashin cudanya yayin gudanar da hidimominsu.

Ga dai hotunan wasu kasuwanni da wuraren a Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Hotunan yadda titunan Kano suna cika da mutane bayan sassauta dokar kulle
Hotunan yadda titunan Kano suna cika da mutane bayan sassauta dokar kulle. Hoto daga Daily Trust/Sani Maikatanga
Asali: UGC

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel