Akwai yiwuwan a gudanar da Hajjin bana amma Saudiyya muke saurara - Hukumar NAHCON

Akwai yiwuwan a gudanar da Hajjin bana amma Saudiyya muke saurara - Hukumar NAHCON

Shugaban hukumar jin dadin alhazan Najeriya, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya ce hukumar na sauraron matsayin kasar Saudiyya ne kafin ta sanarwa yan Najeriya ko Hajjin bana zai yiwu.

Ya ce akwai yiwuwan gudanar da Hajjin bana duk da tsoron da cutar Coronavirus ta jefa cikin zukatan al'umma.

Amma idan haka ya yiwu, zai zo da wasu matakai masu tsaurin gaske domin karin lafiyan Mahajjata.

Ya ce idan haka ya faru, da yiwuwan a rage adadin maniyyatan kasashe.

A jawabin da mataimakin diraktan labarai na hukumar NAHCON, Mousa Ubandawaki, ya saki, ya ruwaito Hassan ya bayyana hakan ne a hirar yanar gizon da kungiyar kamfanonin safarar maniyattan Najeriya.

Akwai yiwuwan a gudanar da Hajjin bana amma Saudiyya muke saurara - Huukumar NAHCON
Huukumar NAHCON
Asali: UGC

KU KARANTA: Mun gama sulhu da yan bindiga a jihar Katsina, mayaudara ne - Gwamna Masari

Yace: "Gwamnatin kasar Saudiyya kadai ce za ta iya yanke shawara ta karshe. Duk abinda zamu yanke na dangane da abin da Saudiyya ta yanke."

Yace da yiwuwan kasar Saudiyya ta amince a gudanar da Hajjin bana saboda matakan da take dauka wajen hana yaduwar cutar COVID-19 da kuma adadin masu samun waraka a kasar kullum.

Daga cikin alamun Hajjin bana zai gudana da ya hararo sune bude Masallatai, sassauta dokokin hana fita, sanya na'urorin tsaftace jiki a kofofin shiga Masallatu da kuma adadin masu waraka daga cutar a kulli yaumin.

Sauran alamun sune raguwar adadin masu kamuwa da cutar a kasar da kuma bude sabbin dakunan gwaji 6.

A bangare guda, Legit.ng ta kawo rahoton cewa Sarkin kasar Saudiyya, Malik Salman Ibn AbdulAziz ya bada umurnin bude Masallacin Manzon Allah S.A.W dake Madina fari daga ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2020.

An fara bari mutane suna shiga amma da sharrudan kare kai daga cutar Coronavirus. A ranar farko da aka bude Masallacin, kimanin mutane 93,774 suka hallarci khamsu Salawati.

Amma har yanzu ba'a bude Masallacin Harami ba. A yau Laraba kadai, an samu sabbin mutane 279 da suka kamu da cutar a Makkah.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel