Mun gama sulhu da yan bindiga a jihar Katsina, mayaudara ne - Gwamna Masari

Mun gama sulhu da yan bindiga a jihar Katsina, mayaudara ne - Gwamna Masari

- Gwamnatin jihar Katsina ta nuna bacin ranta kan rashin cika alkawarin yan bingidan da suka addabi al'ummar jihar

- Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ya rantse ba za sake shiga sulhu da yan bindigan ba

- Wasu yan bindigan daga jihar Zamfara, Kaduna da kasar Nijar suke zuwa, cewarsa

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce ba zasu sake wani sulhu da yarjejeniya da yan bindiga ba a jihar tunda suka saba wanda akayi da su a baya.

Ya ce gwamnatin jihar ta yi yarjejeniya da yan bindigan kuma sun yi alkawarin tuba tare da fita daga jihar amma basu cika alkawarin ba. Mayaudara ne, a cewarsa.

Yayinda yake hira da BBC Hausa a Instagram, gwamnan ya ce daga wasu cikin yan bindigan, suna zuwa ne daga jihar Kadina, Zamfara, har ma daga kasar Nijar.

Masari ya ce shine gwamna na farko da ya fara sulhu da yan bindiga a shekarar 2016 kuma sun fara cika alkawari kafin kuma suka yaudari gwamnati.

Yace: "Mun zabi yin yarjejeniya da yan bindigan ne domin kiyaye asarar rayuka da dukiya amma hakan bai haifi da mai ido ba. Yanzu zamu mika lamarin ga jami'an tsaro."

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da isasshen jami'an tsaro da kayan aiki saboda a samu nasarar yaki da barandanci a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel