Da duminsa: An sallami mutane 292 da suka dawo gida daga Saudiyya bayan makonni 2 a killace

Da duminsa: An sallami mutane 292 da suka dawo gida daga Saudiyya bayan makonni 2 a killace

Gwamnatin tarayya, a ranar Laraba ta sallami wasu yan Najeriya 292 da aka killace a wani Otal a Abuja na tsawon mak biyu bayan dawowarsu daga kasar Saudiyya

An killace su ne don tabbatar da cewa basu kwashi cutar daga kasa Saudiyya ba, kuma hakan an cikin sharrudan da gwamnati ta gindaya.

Amma bayan gwajin da akayi musu bayan karewar wa’adin kwanaki 14, an tabbatar da cewa basu da cutar kuma tuni an sallamesu.

A cewar rahoton The Nation, yawancinsu sun kama hanyan tafiya Jihar Legas.

KU KARANTA: Kotu tayi watsi da karar zargin da akewa tsohon shugaban Kwastam, Dikko Inde, na almundahanan N1.1bn

A ranar Talata, 5 ga watan Mayun 2020, Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na fara kwaso 'yan Najeriya da suka kasa dawo gida a wasu kasashen ketare sakamakon hana zirga-zirga da annobar korona ta janyo.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce za a killace dukkanin mutanen da za a kwaso yayin shigowarsu Najeriya har na tsawon kwanaki 14 domin a tabbatar ba sa dauke da kwayoyin cutar korona.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta nuna cewa, za a kwaso tawagar farko ta 'yan Najeriya 265 a jirgin saman Emirates daga Dubai a ranar Laraba, 6 ga watan Mayu.

Daga baya, ma'aikatar ta sanar da cewa 'yan Najeriya da za su dawo daga kasashen ketare za su biya kudin killacesu da za a yi, kamar yadda sabbin tsarin suka bayyana.

Gabanin sanarwar, wadanda za su iso daga kasashen ketaren ana bukatar su biya kudin jirginsu ne kadai yayin da gwamnati za ta dauki nauyin killace su da za a yi na makonni biyu.

Gwamnati ta sanar da hakan yayinda ta lura cewa ba za ta iya daukar dawainiyar masu dawowa gida ba.

A kalla akwai 'yan Najeriya 4,000 da suka bayyana bukatar su ta dawowa gida Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel