COVID-19: 'Yan kungiyar Barcelona 5 sun kamu da korona

COVID-19: 'Yan kungiyar Barcelona 5 sun kamu da korona

'Yan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona biyar da masu horar da yan wasu biyu sun kamu da coronavirus a farkon lokacin da annobar da bulla.

Tawagar 'yan wasan sun fara atisaye a ranar Litinin da niyyar fara buga wasanni nan ba da dadewa ba kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ana sa ran Real Madrid za su kara da Real Mallorca a ranar 13 ga watan Yunin shekarar 2020.

A halin yanzu dai rahotanni sun nuna cewa dukkan yan tawagar kungiyar lafiyarsu kalau kuma ba su dauke da cutar amma RAC1 ya bayyana cewa mutum bakwai a kungiyar sun kamu da cutar a cikin watanni kadan da suka shude.

COVID-19: 'Yan kungiyar Barcelona 5 sun kamu da korona
COVID-19: 'Yan kungiyar Barcelona 5 sun kamu da korona
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Kotu ta tsare mutumin da ya yi zina da surukarsa

A farkon bullar annobar, kasar SPain wacce ke cikin kasashen da cutar ta yi wa illa sosai a duniya, Barcelona ta yi wa yan kungiyar ta gwaji an kuma gano yan wasa 5 da masu horaswa biyu sun kamu duk da cewa basu nuna alamomi ba.

Kungiyar ba ta bayyana cikaken bayanan wadanda suka kamu da cutar ba kuma ba a saka a cikin rahoton La Liga ba sai dai an ce kowa ya warke kuma ya koma aiki.

Mai tsaron baya Samuel Umtiti ya dawo filin wasa a ranar Litinin bayan raunin da ya yi a farkon kakan wasan bana.

Ansu Fati shi kuma har yanzu yana fama da rauni a gwiwarsa. Mai buga wasan tsakiya Monchu shima yana fama da ciwon cinya har yanzu Ousmane Dembele baya nan.

A halin yanzu Barcelona suna gaba da Real Madrid da maki biyu kuma za su samu damar kara tazarar idan suka yi nasara a kan Mallorca.

Real Madrid ba za su buga wasa ba sai ranar Lahadi inda za su fafata da Eibar a filin wasa ta Alfredo Di Stefano da ke Ciudad Real Madrid.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164