Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)

Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya dakatar da dukkan ma’aikatan da gwamnati ke biya na babban asibitin garin Ngala da ke jihar Borno.

Ma’aikatan sun hada da likitoci, malaman jinya, masu hada magani da masu gwaji na asibitin.

Wannan dakatarwar ya biyo bayan ziyarar ba-zata da ya kai asibitin da karfe 11 na safiyar ranar Litinin.

Duk da karbar albashin da suke yi, ya tarar da cewa ma’aikatan sun bar asibitin a hannun wata kungiyar taimakon kai da kai wacce ke kula da majinyatan, wadanda ‘yan gudun hijira suka fi yawa a ciki.

Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)
Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)
Asali: Facebook

Ngala ita ce hedkwatar karamar hukumar Ngala ta jihar Borno. Garin na yankin iyakar Borno da jamhuriyar Kamaru, Chadi, Sudan da Afrika ta tsakiya.

Bayan kwato garin da aka yi daga hannun mayakan ta’addancin Boko Haram a 2015, Ngala ta kasance masaukin dubban ‘yan gudun hijira. Sun samu mafaka ne a kauyuka da gonaki sakamakon harin ‘yan ta’addan.

Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)
Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)
Asali: Facebook

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Babban asirin Boko Haram ya tonu a Borno - DHQ

Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)
Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)
Asali: Facebook

Kamar yadda Zulum ya saba, ya kai ziyarar ba-zata don gano halin da ma’aikatar lafiya ke ciki a jihar.

Gwamnan ya nuna matukar damuwarsa ta yadda ya tarar da cewa ma’aikatan gwamnatin basu iso ba har karfe 11 na safe.

Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)
Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)
Asali: Facebook

A takaice, shugaban kungiyar da ke kula da asibitin ne ya karba Zulum bayan isarsa.

A fusace Zulum ya ce, “Wannan asibitin gwamnatin jihar Borno ne amma ban tarar da ko ma’aikaci daya na jihar ba duk da muna biyansu albashi a kan lokaci.

“Kungiyar fi360 ce take kula da asibitin wadanda ya kamata su taimaka wa ma’aikatan. Ina umartar hukumar kula da asibitoci da ta datse biyan ma’aikatan asibitin.

“Zan dawo don ganin yadda ayyuka ke tafiya daga baya. Ina fatan ganin akasin hakan.”

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jagoranci raba kayayyakin abinci da wadanda ba na abinci ba ga gidaje 10,000 a Rann, hedkwatar Kala-Balge.

Wannan ziyarar ce ta hudu da gwamnan ke kai wa karamar hukumar da ke da iyaka da jamhuriyar Kamaru.

Jirgin dakarun sojin saman Najeriya ne ya dauka Zulum daga Maiduguri zuwa Rann a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel