Karfin hali: Kotu ta garkame matashin dan shekara 18 da ya shiga ofishin yan sanda ya saci abubuwa

Karfin hali: Kotu ta garkame matashin dan shekara 18 da ya shiga ofishin yan sanda ya saci abubuwa

Kotun Majistaren jihar Osun dake Ile-Ilfe ta bada umurnin garkame wani matashi dan shekara 18, Oladoyin Taiwo, da ya shiga ofishin yan sanda satan Atamfa da kudade.

Lauyan hukumar, Sunday Osanyintuyi, ya laburtawa kotu cewa Taiwo ya aikata laifin ne ranar 15 ga Mayu, 2020 misalin karfe 9 na dare a ofishin yan sandan Moore dake garin Ili-Ife.

Taiwo ya fasa ofishin Sifeto Vitowani Bukola ne ta kofa inda ya saci kudi N4,000.

Hakazalika ya dauke fanka, buhun shinfaka, na'urar DVD, Antenan GOTV, Socket da kuma kudi N25,300.

Bugu da kari, ya dauke Atamfa yadi 12 na wata mata.

Lauyan yace: "Ya kara satan atamfa yadi 12 mai kimanin kudi N14,000, mallakin wata Adetutu Osideru."

Lauya Osanyintuyi ta bayyanawa kotu cewa hakn ya sabawa dokokin jihar masu lamba 383, 390(9) da 41.

A bangare shi kuma barawon, ya amsa laifinsa kan zargi hudu da akayi masa.

Lauyan matashi, Innocental Akhigbe, ta roki kotu ta baiwa matashin beli.

Amma Alkalin majistare, Joseph Owolawi, ya ki bayar da belin kuma ya bada umurnin garkameshi a caji ofis da hukumar yan sanda zuwa ranar 6 ga Yuni da za'a dawo shari'a domin duba yiwuwan bashi beli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel