Coronavirus: Jerin jihohi 8 da aka fi samun mutuwa da jihohi 7 da babu mutuwa har yanzu

Coronavirus: Jerin jihohi 8 da aka fi samun mutuwa da jihohi 7 da babu mutuwa har yanzu

Cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus (COVID-19) ta hallaka akalla mutane 380,000 a fadin duniya kuma har yanzu bata daina katse rayuka ba.

Yayinda wasu kasashe suka samu daman shawo kanta, wasu na fama da ita musamman nahiyar Afirka da Amurka ta kudu.

A nahiyar Afrika, akalla mutane 4,467 suka mutu kuma kasar Algeriya, Kamaru, Najeriya, Misra, Afrika ta kudu, Maroko da Sudan suka yi rashi mafi yawa.

A nan gida Najeriya, cutar ta hallaka mutane 314 a jihohi 29 kawo ranar Laraba, 3 ga watan Yuni, 2020, bisa alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, watau, NCDC.

Legit.ng Hausa ta kawo muku jerin jihohin Najeriya takwas da suka fi adadin wafati da kuma jihohi bakwai da suka samu nasarar rashin samun mutuwa sakamakon cutar ko daya.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta zaftare kasafin kudin Ma'aikatar Lafiya da ta Ilimi

Ga jerin jihohin da aka fi samun mutuwa da adadin wadanda suka mutu:

1. Jihar Legas (67)

2. Jihar Kano (45)

3. Jihar Borno (26)

4. Birnin tarayya Abuja (20)

5. Jihar Katsina (19)

6. Jihar Rivers (16)

7. Jihar Edo (14)

8. Jihar Sokoto (14)

Ga jerin jihohin ba'a samun mutuwa ba:

1. Jihar Ebonyi

2. Jihar Imo

3. Jihar Taraba

4. Jihar Enugu

5. Jihar Abiya

6. Jihar Kogi

7. Jihar Benue

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel