Buhari yana jagorancin taron FEC ta intanet (Hotuna)

Buhari yana jagorancin taron FEC ta intanet (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari a yanzu yana jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Kasa, FEC, a gidan gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.

Taron da aka fara misalin karfe 9:02 agogon GMT ya samu hallarcin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo (SAN), Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Shugaban Maaikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari da wasu ministoci.

Ministocin da suke cikin dakin taron sun hada da ministocin Sharia, Sufurin Jiragen Sama, Kudi, Sadarwar, Muhalli, Albarkatun Ruwa, Tsaro da kuma Ayyuka.

DUBA WANNAN: Kotu ta tsare mutumin da ya yi zina da surukarsa

Dukkan sauran ministocin kasar suma suna hallartar taron ta intanet daga ofisoshinsu dake babban birnin tarayya, Abuja.

Ana sa ran taron zai mayar da hankali ne wurin tattauna yadda kasar za ta takaita matsalolin da annobar COVID-19 da janyo da kuma yadda za a inganta rayuwar yan Najeriya a cikin wannan lokacin annobar.

Ku biyo mu don samun cikaken rahoton ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel