Gwamnatin Katsina ta yi martani kan kisar hakimin 'Yantumaki

Gwamnatin Katsina ta yi martani kan kisar hakimin 'Yantumaki

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa ya ce kisar gillar da aka yi wa hakimin 'Yantumaki, Abubakar Atiku ba zai sa gwamnatin jihar ta dena yaki da ta ke yi da 'yan bindiga a jihar ba.

A cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Abdullahi Inuwa ya fitar, ya ce wadanda suka aikata wannan mummunan lamari da sauran masu aikata laifuka a jihar za su dandana kudarsu.

Ya yi kira ga al'ummar jihar su bawa gwamnati da hukumomin tsaro goyon baya wurin yaki da batagarin ta hanyar taimaka musu da bayanai masu amfani da zai taimaka wurin magance fitinar.

Gwamnatin Katsina ta yi martani kan kisar hakimin 'Yantumaki
Gwamnatin Katsina ta yi martani kan kisar hakimin 'Yantumaki. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kotu ta tsare mutumin da ya yi zina da surukarsa

Bayan nuna bakin cikinsa bisa afkuwar lamarin da ya yi sanadin mutuwar hakimin, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai son zaman lafiya, aiki tukuru kuma shugaba da ya bayar da gudunmawa wurin ganin an samu zaman lafiya a jihar.

Kazalika, ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan tsohon shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Batsari, marigayi Alhaji Abdulhamin wanda wasu yan bindiga suka kai masa hari suka halaka shi.

Ya kara da cewa yan bindigan uku da suka kashe tsohon shugaban na APC suma sun gamu da ajalinsu a hannun wasu tubabbun 'yan bindigan da ke taimakawa hukumomin tsaro wurin yaki da batagari.

A wani rahoton, mun kawo muku cewa 'yan bindiga a ranar Asabar sun sace dan kasuwa, Yusuf Maifata a gidansa da ke garin Sankara da ke karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Mazauna unguwar sun ce yan bindigan sun isa unguwar ne misalin karfe 1.47 na dare dauke da bindigu suna harbe harbe wadda hakan ya sa mutane suka firgita sannan suka sace Maifata daga gidansa.

Wani daga cikin iyalan dan kasuwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, "Maifata ya dade yana fama da rashin lafiya. An sallamo shi daga asibiti ranar Alhamis yana murmurewa a gida ne sai kwatsam abin ya faru."

Majiyar ya kuma bayyana cewa yan bindigan sun kira iyalansa sun nemi a biya su Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa.

Sun kuma tambayi irin abincin da dan kasuwan ya saba ci da magungunan da asibiti suka rubuta masa ya rika sha.

Yana sume suka tafi da shi saboda firgicin karar harbin bindiga da ya rika ji yayin da ya ke kwance a gadonsa kafin su shiga gidan su dauke shi kamar yadda majiyar ya shaidawa Premium Times.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa, Audu Jinjiri ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Mr Jinjiri ya ce tuni rundunar ta baza jamianta na sashin yaki da masu fashi da makami da garkuwa da mutane su bi sahun yan bindigan domin ceto dan kasuwan mai shekaru 75 da haihuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel