El-Rufai ya shawarci matarsa a kan yadda za ta yi da tsagerun Twitter

El-Rufai ya shawarci matarsa a kan yadda za ta yi da tsagerun Twitter

Matar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai ta nemi wata shawara da ta bar mutane cike da mamaki a shafinta na twitter.

Matar Nasir El-Rufai ta tambaya mabiyanta a shafinta na twitter shawara a kan ta fara rufe tsageru daga shafinta masu bibiyarta a kafar sada zumuntar ko a'a.

"In hana su ganin shafi na ta hanyar rufesu ko a'a?", wannan ce tambayar da ta yi a shafinta.

Amma babban abun mamakin shine yadda Gwamna Nasir El-Rufai ya yi martani.

Ya ce: "Kada ki karramasu ta hanyar rufe su kwata-kwata, ki dakatar da kanki daga ganinsu ne, ta yadda za su yi ta ihunsu ba tare da kin san suna yi ba!"

El-Rufai ya shawarci matarsa a kan yadda za ta yi da tsagerun Twitter
El-Rufai ya shawarci matarsa a kan yadda za ta yi da tsagerun Twitter. Hoto daga shafin LindaIkeji
Asali: Twitter

Tambayar Hadiza ta zo ne kwanaki kadan bayan da ta yi murnar samun mabiya dubu tamanin a shafinta na twitter.

Hakan kuwa ta faru ne bayan da ake ta zantuka a kan kashe-kashen da ya ta'azzara a yankin kudancin Kaduna da ke arewa maso yammacin jihar.

An zargi matar gwamnan da nuna halin ko in kula a kan kashe-kashen da ke aukuwa a jihar.

El-Rufai ya shawarci matarsa a kan yadda za ta yi da tsagerun Twitter
El-Rufai ya shawarci matarsa a kan yadda za ta yi da tsagerun Twitter. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bude kasuwanni da wuraren bauta: El-Rufai ya bada sanarwa

A wani labari na daban, Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, ya ce bai taba karbar cin hanci ko bukatar hakan ba.

Ya kalubalanci duk wanda ke da wani bayani mabanbancin hakan da ya fito ya bayyana.

A ranar Litinin, Sirika ya ce wannan bayanin ya zama dole sakamakon caccakarsa da 'yan Najeriya ke yi a Twitter.

Sun zargi ma'aikatar sufurin jiragen saman da bukatar cin hanci kafin su amince da tashin jiragen sama yayin barkewar annobar nan.

A yayin jawabi ga kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona a Abuja, ya ce wannan ikirarin ba gaskiya bane.

"Na karanta a shafin Twitter cewa akwai wasu kudi da muke karba kafin amincewa da tashin jiragen sama. Wannan al'amari ya nisanta daga gaskiya. Kyauta ne kuma amince wa ake yi," yace.

Ministan ya shawarci 'yan kasa da su daina rayuwar tuna baya don kuwa gwamnatin Buhari ta bambanta daga ta sauran.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel