Karin mutum 241 sun harbu da korona a Najeriya, jimilla 10819
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 241 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.52 na daren ranar Talata, 2 ga watan Yuni na shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 241 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;
Lagos-142
Oyo-15
FCT-13
Kano-12
Edo-11
Delta-10
DUBA WANNAN: Kotu ta tsare mutumin da ya yi zina da surukarsa
Kaduna -9
Rivers-9
Borno-8
Jigawa-4
Gombe-3
Plateau-3
Osun-1
Bauchi-1
Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Talata 2 ga watan Yunin 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 10819.
An sallami mutum 3239 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 314.
A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba sun harbe hakimin 'Yantumaki har lahira a jihar Katsina, Abubakar Atiku Maidabino a fadarsa a safiyar ranar Litinin.
Wata majiya daga garin ta shaidawa Daily Trust cewa 'yan bindigan sun taho a babura ne misalin karfe 12 na dare inda suka rika harbe harbe a iska domin razana mutanen kauyen.
Daga bisani yan bindigan sun shiga cikin fadar suka kashe hakimin nan take kuma suka raunata daya daga cikin masu gadinsa.
Za a yi janai'zar mammacin misalin karfe 11 na safe a fadarsa bisa koyarwan addinin musulunci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng