Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)

Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jagoranci raba kayayyakin abinci da wadanda ba na abinci ba ga gidaje 10,000 a Rann, hedkwatar Kala-Balge.

Wannan ziyarar ce ta hudu da gwamnan ke kai wa karamar hukumar da ke da iyaka da jamhuriyar Kamaru.

Jirgin dakarun sojin saman Najeriya ne ya dauka Zulum daga Maiduguri zuwa Rann a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2020.

Gwamnan da ya yi irin tafiyar har sau uku, na farko a watan Yunin 2019, kwanaki kadan bayan hawansa mulkin jihar don duba yanayin ayyukan da ake yi a yankin.

Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Asali: Facebook

A watan Disamban 2019, ya koma garin inda ya raba wa mata masu takaba kudi N15,000 kowannensu.

Zulum ya sake komawa Kala-Balge a watan Fabrairun shekarar nan don raba naira miliyan 100 ga iyalai 10,000 da ke yankin.

A yayin wannan ziyarar da ya kai ta ranar Lahadi, Zulum ya duba yadda ake raba kayan tallafin ga mata da kuma maza, tare da 'yan Najeriya 300 da ke jamhuriyar Kamaru.

Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Asali: Twitter

Kowanne daga cikin jama'ar ya samu buhun masara mai nauyin 50kg, katan din taliya, buhunan shinkafa biyu da kuma lita uku na man girki.

An kara wa matan da turamen atamfofi bayan basu kayan abincin.

Mazauna Rann sun dade suna fama da rashin titi mai kyau tun bayan da ruwa ya yi wa hanyar barna. Wannan ne yasa mazauna garin suka nemi mafaka a jamhuriyar Kamaru.

Bayan jawabin Gwamna Zulum, ya jinjinawa ma'aikatar jin kai da walwalar 'yan kasa, hukumar habaka yankin arewa maso gabas da kuma hukumar tallafin gaggawa tare da gidauniyar Dangote.

Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Asali: Facebook

KU KARANTA: Bude kasuwanni da wuraren bauta: El-Rufai ya bada sanarwa

Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Asali: Facebook

Ya ce: "Ina amfani da wannan damar wajen mika godiyata ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan kokarin da yake yi wa yankin arewa maso gabas.

"Ina mika godiyata ga ma'aikatar walwala da jin kan 'yan kasa, hukumar habaka yankin arewa maso gabas, NEMA da kuma gidauniyar Dangote a kan gudumawar da suka bada."

Bayan kammala rabon kayayyakin, Gwamnan Zulum ya karasa Wulgo don duba yanayin barnar da mayakan Boko Haram suka yi wa yankin.

Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Asali: Facebook

Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Asali: Facebook

Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Borno: Zulum ya mika tallafi ga gidaje 10,000, ya kai wa soji ziyara (Hotuna)
Asali: Facebook

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, duba Wulgo da yayi na nufin za a gyara ta don tabbatar da komawar masu gudun hijirar da suka tsere daga yankin, a halin yanzu suka sansani a Gamboru Ngala.

Gwamnan ya kwana a Gamboru Ngala, inda ya samu fuskanta tare da tattaunawa da 'yan gudun hijira.

A yayin ziyarar, Gwamna Zulum ya ziyarci wurin da dakarun sojin Najeriya suke don karfafa musu guiwa.

Ya ba su buhu 250 na shinkafa mai nauyin 50kg, buhu goma na sukari mai nauyin 50kg, kwali 200 na indomi, kwali 500 na taliya, man girki da kuma kudi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel