Ba da izini na aka saki takardun nan ba - Tsohon saurayin amaryar Hameed Ali ya yi bayani

Ba da izini na aka saki takardun nan ba - Tsohon saurayin amaryar Hameed Ali ya yi bayani

Zubairu Malami, tsohon saurayin Zainab Yahaya, sabuwar amaryar Hameed Ali, kontrola janar na hukumar hana fasa kwabri watau kwatsam, ya yo tsokaci kan takardun neman kudin da ya yadu a soshiyal midiya.

Hameed Ali, wanda shugaban Muhammadu Buhari ya nada a 2015 da ya auri Zainab ne ranar Asabar, shekaru biyu bayan mutuwar matarsa ta farko, Hadiza Jummai.

A ranar Litinin, Takardun lauyoyi sun bayyana yadda Zubairu Malami ya lissafa kudade kimanin N9m da ya kashewa Zainab Yahaya a matsayin saurayinta amma ta yaudareshi ta auri wani.

Ya yi barazanar kai Zainab kotu idan taki dawo masa da kudaden da ya kashe mata.

Amma a wasikar da TheCable ta samu ranar Talata, Zubairu Malami, ya ce ba da izininsa aka saki wannan takardar ba.

Ya yi san barka kan aurenta kuma ya bayyana cewa tuni ya rungumi kaddarar Allah bai yi zasu auri juna ba.

Yace: "Ni, Zubairu Dalhatu Malami, na gida mai lamba 224 Durumin Zungura, jihar Kano, ina mai sanar da daukacin al'umma cewa takardar da aka yada a Sahara Reporter da wasu jaridu ba da izinina aka wallafa ba."

"Zainab Abdullahi Yahaya tsohuwar budurwata ce da nayi niyya aure, amma Allah madaukaki bai kaddara hakan ba tunda ta auri wani."

"Saboda haka, ina mata fara Allah ya basu zaman lafiya da albarka."

Ba da izini na aka saki takardun nan ba - Tsohon saurayin amaryar Hameed Ali ya yi bayani
Hameed Ali
Asali: Twitter

KU KARANTA: Majalisar wakilan tarayya ta amincewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, karban bashin $22.7bn daga kasar waje

Daga cikin kudin da Zubairu ya ce ya kashe akwai jarin wasu kaya daga Amurka na N450, 000. N2, 778, 207. 48 zuwa kasashen Saudi da Dubai da Sin da aron jarin N1, 500, 000.

Haka zalika ya ce ya ba ta N280, 000 domin ta kama wani shago a birnin Kano, sannan da wasu N350,000 da ta ba mahaifinta. Har ila yau ya ce ta karbi kudin haya na N350, 000.

Zubairu ya na ikirarin kashe N1.7m a kan lefe, N300, 000 wajen sayen lullubai, da wasu N360, 000 wajen keta hazo zuwa kasar Sin. Haka zalika ya bata N500, 000 domin ta saye mota.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel