Buhari ya yi magana a kan kisan matashiya a cikin Coci

Buhari ya yi magana a kan kisan matashiya a cikin Coci

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika sakon ta'aziyya ga dangin matashiyar dalibar nan, Uwaila Omozuwa, wacce aka kashe ta hanyar yi ma ta fyade a cikin coci a jihar Edo.

A takaitaccen sakon da ya wallafa a shafinsa na tuwita, shugaba Buhari ya bukaci rundunar 'yan sanda ta gaggauta gudanar da bincike tare da zakulo wadanda su ka yi wa matashiyar kisan gilla.

"Ina mai mika sakon ta'aziyya ga dangi da abokan Uwaila Omozuwa. Ina kira ga rundunar 'yan sanda ta Najeriya a kan ta hanzarta yin bincike tare da zakulo duk wani mai hannu a cikin lamarin domin tabbatar da cewa an gurfanar da su a gaban shari'a," a cewar shugaba Buhari.

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Edo ta sanar da cewa ta kama wani da ake zargin ya na da hannu a kisan Omozuwa.

A cewar Chidi Nwabuzor, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, an kama mutumin ne bayan zanen yatsunsa sun fito a jikin tukunyar gas da aka yi amfani da ita wajen kisan matashiyar.

Rundunar 'yan sanda ta ce an kaiwa Omozuwa farmaki ne yayin da ta ke karatu a cikin Cocin RCCG (Redeemed Christian Church of God), da ke birnin Benin.

Buhari ya yi magana a kan kisan matashiya a cikin Coci
Omozuwa
Asali: UGC

Matashiyar, mai shekaru 22, ta mutu a cikin kwana na uku bayan an kaita asibiti domin ceto rayuwarta, kamar yadda Olaitan Olubiyi, kakakin Cocin, ya sanar.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana kisan Omozuwa a matsayin mugunta tare da daukan alkawarin kama ma su hannu a kisanta nan bada dadewa ba.

DUBA WANNAN: Kotu ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan matashin da ya kashe mahaifinsa

Olubiyi ya ce Omozuwa, mamba a kungiyar mawakan Cocin, kan ziyarci Cocin domin yin karatu da nazarin wakokin yabo.

Ya kara da cewa hakan ya zamar ma ta tamkar al'ada tun bayan saka dokar kulle a watan Maris.

"Mutuwarta ta girgizamu matuka. Tun da aka saka dokar kulle ta ke zuwa ta karbi makullin Coci kowacce rana a wurin Fasto domin ta yi karatu da nazari, idan ta kammala ta dawo ma sa da makullin.

"Amma a wanna rana ba ta mayarwa da Fasto makulli ba kamar yadda ta saba. Sai da maigadin dare ya zo, sai ya isketa cikin jini, rabin jikinta tsirara," a cewar Olubiyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel