Bude wuraren bauta: Sharudda 17 da aka gindaya wa masallatai a FCT

Bude wuraren bauta: Sharudda 17 da aka gindaya wa masallatai a FCT

Hukumomin babban birnin tarayyar Abuja sun saka wa masallatai sharudda da ake bukatar su kiyaye kafin taruwar jama'a domin ibada.

A ranar Litinin da ta gabata, gwamnatin tarayya ta dakatar da haramcin tarukan ibada bayan rufe masallatai da coci don hana yaduwar cutar korona.

Amma kuma, duk da sanarwar bude wuraren ibada da gwamnatin tarayya ta yi, abubuwa basu daidaita ba sakamakon sabbin matakan da hukumomi suka gindaya kafin bude wuraren ibadar.

A babban masallacin kasa na Abuja, hukumar ta sanar da BBC cewa sai nan gaba za a dawo da harkokin bauta.

Amma kuma an gindaya wa wasu masallatan da aka bude sharudda a garin don dakile yaduwar cutar.

Ga sharuddan kamar haka:

1. Dole ne a bude masallaci minti 20 kafin fara sallah sannan a rufe shi bayan minti 20 da gudanar da sallah.

2. Ana son bada tazara tsakanin mutane da za su jira sallar Isha'i bayan Magriba a cikin masallaci.

3. Adadin lokacin gudanar da sallar Juma'a tare da huduba kada ta wuce awa daya.

4. Ba a yarda a gudanar da wata sallah a cikin masallaci ba bayan sallar Juma'a.

5. An haramta wa wadanda suka haura shekaru 65 da kuma masu fama da cututtuka masu hatsari zuwa masallacin.

Bude wuraren bauta: Sharudda 17 da aka gindaya wa masallatai a FCT
Bude wuraren bauta: Sharudda 17 da aka gindaya wa masallatai a FCT. Hoto daga BBC
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Ikon Allah: Yadda aka samu shugabannin kasa 2, gwamnoni 4 da ministoci 2 a aji daya

6. An gindaya sharadin dauke littatafai daga masallatai na wani lokaci.

7. Dole ne amfani da takunkumi ga duk wanda zai shiga masallaci.

8. Dole ne tsaftace masallatai kafin lokutan sallah ballantana amfani da sinadarin goge shimfidu.

9. Samar da na'urorin auna dumin jiki da kuma samar da sinadarin tsaftace hannu kafin shiga masallaci da makewayi.

10. Kada lokacin kiran sallah da tsayar da ikamah ya wuce minti 10.

11. Bude kofa da tagogi a duk lokutan gudanar sallolin farilla da sallar Juma'a dole ne.

12. Duk mai zuwa masallaci ya zo da dardumarsa ta sallah.

13. Ana bukatar bada tazarar a kalla mita biyu a tsakanin sahu.

14. Yawan masu sallah kada ya zarce daya bisa uku na mutanen da masallacin zai iya dauka.

15. Ba a bukatar masallata su dinga gaisawa ko rungumar juna.

16. A dinga rubuta sunaye kafin shiga masallaci domin gudanar da salloli biyar na farilla.

17. Makarantun islamiyyu za su ci gaba da kasancewa a garkame.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel