Yanzu-yanzu: Yan majalisa sun amincewa Buhari ya karbo bashin $22.7bn
Majalisar wakilan tarayya ta amincewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, karban bashin $22.7bn daga kasar waje.
Yan majalisar sun amince da karbo bashin ne a zaman majalisan da ya gudana ranar Talata bayan samun rahoton kwamitin basussuka.
Za ku tuna cewa lokacin da shugaba Buhari ya mika bukatar karban bashin a 2019, ya ce za'ayi amfani da su wajen wasu manyan ayyuka don jin dadin al'umma. TheCable ta hararo.
Amma wasu yan majalisa musamman daga yankin kudu maso yamma (Kasar Igbo) sun nuna rashin amincewarsu da hakan inda suka yankinsu ba ta da rabo a ayyukan da za'ayi da kudi.
Hakan ya kai ga dakatad da lamarin bashin, sai yanzu aka samu daman cigaba bayan da Kakakin majalisan, Femi Gbajabiamila, ya roke su.
Gbajabiamila ya ce duk matakan da suka dauka na ganin cewa an magance matsalolin sun gamu da cikas saboda an riga an kammala yarjejeniya da wadanda zasu bada bashin.
"Saboda haka imma mu amince da shi gaba daya, ko kuma kada mu amince da shi gaba daya." Yace

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Ba zamu iya sayar da litan man fetur N121.5 ba - Yan kasuwan mai
Kakakin ya kara da cewa majalisar ta samu nasarar yarjejeniya da fadar shugaban kasa cewa idan za'a karbi wani bashin gobe, wajibi ne a sanya yankin kudu maso gabas da Arewa maso gabas ciki.
"A karon farko, mun ayyana ayyuka na musamman da za a yi. Mun yi yarjejeniya da bangaren zartarwa kan cewa wajibi ne a sanya wadannan ayyuka a wani sabon bashin da za a karba." Yace
Shugaba Buhari ya mika bukatar karban bashi ne ga majalisar dokokin tarayya karkashin Bukola Saraki amma sukayi watsi da shi.
A bangare guda, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa masu zanga-zanga a karkashin kungiyar Concerned Citizens of Abia North daga jihar Abia a ranar Talata, sun mamaye majalisar dokokin tarayya.
Sun yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da ya yi gaggawan sanya kujerar bulaliyar masu rinjaye a majalisar, Sanata Orji Uzor Kalu a kasuwa.
Yan mintuna bayan zanga-zangar, kotu ta bada umurnin sake Sanata Orji Kalu daga kurkuku. Hakan na nufin cewa za koma kujerarsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng