Kotu ta ba da umarnin sakin Orji Kalu daga kurkuku

Kotu ta ba da umarnin sakin Orji Kalu daga kurkuku

A ranar Talata, 2 ga watan Yuni, wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Legas, ta ba da umarnin sakin tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, daga kurkuku.

A ranar 5 ga watan Dasumba, 2019, aka yankewa Mista Kalu hukuncin daurin na shekaru 12 a gidan dan Kande.

Hakan ya biyo bayan samunsa da laifin yin ruf da ciki a kan N7.1bn tare da kamfaninsa, Slok Nigeria Limited, da kuma wani tsohon Daraktan Kudi a gwamnatin Jihar Abia, Jones Udeogu.

Haka kuma Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, masu zanga-zanga a karkashin kungiyar al'umma masu kishi reshen Abiya ta Arewa, a yau Talata sun mamaye majalisar dokoki ta Tarayya.

Sun yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da ya yi gaggawar sanya kujerar bulaliyar masu rinjaye a majalisar, Sanata Orji Uzor Kalu a kasuwa.

Mista Kalu ya kasance dan jam’iyya mai ci ta APC kuma har yanzu shi ne Sanata mai wakilcin shiyar Abia ta Arewa a zauren majalisar dattawa.

Sanata Orji Uzor Kalu
Sanata Orji Uzor Kalu
Asali: UGC

A cewar kungiyar, sanya kujerar a kasuwa zai sa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gudanar da sabon zabe domin samar da wanda zai wakilci Abia ta Arewa a Majalisar Dattawan.

A ranar Juma'a 8 ga watan Mayu, Kotun Kolin Najeriya ta soke hukuncin daurin shekara 12 da aka yanke wa tsohon gwamnan na jihar Abia.

KARANTA KUMA: IPMAN ta umarci 'yan kasuwa su siyar da mai a kan N123.50 duk lita

Kotun Kolin, wacce ta soke hukuncin yayin bayyana dalilinta ta bayyana cewa, alkalin da ya yanke hukuncin ba shi da hurumin yi wa tsohon gwamnan shari'a.

Ta na mai cewa, "Mai Shari'a Mohammed Idris na kotun tarayya ta Legas da ya yanke hukuncin, an riga an daga likafarsa zuwa matsayin alkalin Kotun Daukaka Kara ta kasar, don haka ba shi da hurumin yanke hukunci kan shari'ar Mr Kalu."

Fitar wannan hukunci ke da wuya, hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya wato EFCC, ta ce tana da ja kuma ba za ta bari hakan ta sabu ba.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta yi allawadai da hukuncin sannan ta ce "za ta koma fagen daga don ganin an hukunta tsohon gwamnan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel