Adadin masu cutar korona a Afirka ya zarta 150,000 - WHO

Adadin masu cutar korona a Afirka ya zarta 150,000 - WHO

- Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce an samu mutum fiye da mutum 150,000 da suka kamu da Coronavirus a nahiyar Afirka

- Hukumar ta ce fiye da mutum 63,000 sun warke yayin da 4,200 suka mutu sakamakon annobar

- Rahoton da WHO ta wallafa ya nuna cewa mutum 34,357 sun kamu a Afirka ta Kudu, 10, 578 a Najeriya, sai 9,513 a Algeria

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, ta sanar da cewa adadin mutanen da cutar korona ta harba a nahiyar Afirka sun haura 150,000.

Reshen Hukumar WHO na Afrika da ke birnin Brazzaville a kasar Congo, shi ne ya fitar da wannan sanarwa a kan shafin dandalin sada zumunta na Twitter.

Sanarwar ta bayyana cewa, cutar korona ta harbi fiye da mutum 150,000 a nahiyar Afirka, kuma an samu sama da mutum 63,000 da suka warke bayan kamuwa da cutar.

Haka kuma alkaluman da Hukumar ta fitar sun nuna cewa, an samu fiye da mutum 4,200 da cutar korona ta hallaka a baki daya nahiyar Afrika.

Kididdigar ta nuna cewa, kasar Afrika ta Kudu, Najeriya da kuma Algeria, sun fi sauran kasashen nahiyar yawan mutanen da cutar ta harba.

Cikin rahoton, Afirka ta Kudu tana da mutum 34,357 da suka kamu da cutar sai kuma mutum 705 wadanda suka mutu.

A Najeriya cutar ta harbi mutum 10, 578, sannan kuma an tabbatar da mutuwar mutum 299 a kasar.

Shugaban Hukumar WHO na Duniya; Tedros Adhanom
Shugaban Hukumar WHO na Duniya; Tedros Adhanom
Asali: UGC

Sai kuma kasar Aljeriya inda alkaluma suka tabbatar da kamuwar mutane 9,513, yayin da mutane 661 suka riga mu gidan gaskiya.

A Ghana an samu mutum 8,070 da suka harbu, sai kuma mutum 36 da cutar ta katsewa hanzari. Kasar Kamaru tana da mutum 6,397 da suka harbu yayin da mutum 191 suka kwanta dama.

KARANTA KUMA: Kotu ta ba da umarnin sakin Orji Kalu daga kurkuku

Kasar Lesotho, Seychelles, da kuma Namibia, su ne kasashe masu mafi karancin mutanen da aka samu sun kamu da cutar a nahiyar.

Mutum biyu kacal aka tabbatar cutar ta harba a kasar Lesotho kuma babu wanda ya rasa ransa. Hakazalika kasar Seychelles inda aka samu mutum 11 da suka harbu ba tare da salwantar rai ko guda ba.

Ita ma kasar Namibia tana da adadin mutum 25 da cutar ta damka, sai dai nan ma ba a samu salwantar rai ko daya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel