IPMAN ta umarci 'yan kasuwa su siyar da mai a kan N123.50 duk lita

IPMAN ta umarci 'yan kasuwa su siyar da mai a kan N123.50 duk lita

- IPMAN reshen jihar Kano ta ba da umarnin a koma siyar da man fetur a kan N123.50 duk lita daya

- Hukumar daidaita farashin man fetur PPPRA ta nemi a koma siyar da man fetur a kan N123.50 ko kuma N121.50 duk lita

- IPMAN ta ja hankalin al'umma cewa wannan ba umarni bane, shawara ce kurum da ta ga za ta iya dauka

Kungiyar manyan dillalan man fetur ta kasa wato IPMAN, ta umarci dukkanin mambobinta da su fara siyar da makamashin man fetur a kan N123.50 duk lita daya.

Hakan ya biyo bayan shawarar rage farashin litar mai a fadin Najeriya daga Naira 125.00 zuwa Naira 121.50 da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Hukumar daidaita farashin man fetur PPPRA ce ta sanar da rage farashin man fetur cikin wasikar da ta aikewa 'yan kasuwar mai a ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2020.

Da ya ke jawabi dangane da lamarin, shugaban kungiyar IPMAN reshen jihar Kano, Bashir Dan-Mallam, ya ce za su dauki shawarar wannan sabon hukunci da PPPRA ta fitar.

IPMAN ta umarci 'yan kasuwa su siyar da mai a kan N123.50 duk lita
IPMAN ta umarci 'yan kasuwa su siyar da mai a kan N123.50 duk lita
Asali: Facebook

A yayin da Hukumar kayyade farashin da ba da shawarar a koma siyar da litar mai daya a kan N121.50 ko kuma N123.50, Dan-Mallam ya ce za su rika siyar da kowace lita daya a kan N123.50.

Sai dai fa ya ce al'umma su sani cewa, wannan kayyade sabon farashi da aka yi a yanzu ba umarni bane, illa iyaka shawara da suka ga za su iya dauka.

KARANTA KUMA: Shugabannin kasashe 10 da suka fi arziki a tarihin duniya

A sanadiyar haka Dan-Mallam ya nemi dukkan dillalai da ke karkashin jagorancinsa, da su yi riko da sabon farashin, kuma su koma siyar da kowace lita daya a kan Naira 123 da kobo hamsin.

Ya ba da tabbacin cewa, al'umma su sha kuriminsu domin kuwa duk da dagula lamura da cutar korona ta yi a fadin kasar, man fetur zai ci gaba wadata kuma ba zai yanke ba.

Haka zalika ya shawarci al'umma da su ci gaba da zage dantse wajen kiyaye dokoki da matakan da mahukuntan lafiya suka shar'anta domin dakile yaduwar cutar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel