Allah ya yi wa Sanata Munir Muse rasuwa

Allah ya yi wa Sanata Munir Muse rasuwa

Tsohon dan majalisar dattijai mai wakiltan mazabar Legas ta Tsakiya, Munir Muse ya rasu.

Dan sa, Suleiman Muse ne ya sanar da rasuwar dan majalisar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Da ya ke sanar da rasuwar mahaifinsa, Suleiman ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tausayi da jin kai.

Tsohon sanatan Najeriya, Munir Muse ya rasu
Tsohon sanatan Najeriya, Munir Muse ya rasu. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe hakimin 'Yantumaki a Katsina

Ya ce, "Yanzu na yi rashin mahaifi mai tausayi da kulawa, Sanata Munirudeen Adekunle Muse.

"Nayi maka ganin karshe a cikin babban masallacin Legas. Ban san cewa daga lokacin ba zan sake ganin ka da rai ba."

"Na kira ka a waya Jumaa biyu da suka shude. Ka kira ni daga baya kuma mun tattauna wasu abubuwa. Ban san bankwana ka ke yi da ni ba."

Majiyar Legit.ng ta gano cewa Muse, tsohon Manajan tashan jirgin Apapa kuma tsohon shugaban karamar hukumar Apapa ya mutu ne a safiyar ranar Talata.

Ya rasu makonni biyu bayan cikarsa shekaru 80 da haihuwa.

Wani jigo a jamiyyar All Progressives Congress, APC, Joe Igbokwe shima ya tabbatar da rasuwar tsohon sanatan a hirar wayar tarho da ya yi da majiyar Legit.ng.

Shugaban jamiyyar APC na jihar Legas, Henry Ajomale shima ya yi tsokaci game da rasuwar tsohon sanatan.

Ya ce, "Mutum ne mai hada kan mutane kuma jagora daga Apapa. Dattijon kwarai ne kuma ginshiki a jamiyyar mu, yana daya daga cikin wadanda suka kafa APC a jihar mu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel