Jerin kananan hukumomi 20 da akafi yawan masu cutar Korona a Najeriya
- Hukumar NCDC ta sakin jerin kananan hukumomin da suka fi yawan masu cutar Coronavirus a Najeriya
- A jerin, kananan hukumomin nan 20 ne kashe 60 cikin 100 na masu cutar suke zaune
- 11 cikin wadannan kananan hukumomin na Jihar Legas
Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, ta saki jerin kananan hukumomin da suka yawan masu dauke da cutar Coronavirus a Najeriya.
The Nation ta ruwaito cewa lissafin fa NCDC ta saki ya nuna cewa wadannan kananan hukumomin 20 ke dauke da kashi 60% na masu cutar Korona a Najeriya.
Najeriya na da kananan hukumomi 774.
Legit.ng ta tattaro cewa 11 cikin wadannan kananan hukumomin na jihar Legas.
KU KARANTA: Yadda aka samu shugabannin kasa 2, gwamnoni 4 da ministoci 2 a aji daya
Ga jerin kananan hukumomi 20 mafi yawan masu cutar COVID-19 a Najeriya:
1. Lagos Mainland council - 1,274
2. Abuja Municipal council - 536
3. Mushin LGA (Lagos) - 458
4. Eti-Osa LGA (Lagos) - 403
5. Tarauni LGA (Kano) - 248
6. Katsina LGA - 242
7. Alimosho LGA (Lagos) - 239
8. Kosofe (Lagos) - 175
9. Dutse (Jigawa) - 170
10. Ikeja (Lagos) - 168)
11. Maiduguri (Borno) - 167
12. Nassarawa - 152,
13. Oshodi/Isolo (Lagos) - 132
14. Apapa (Lagos) - 131
15. Amuwo Odofin (Lagos) - 129
16. Oredo (Edo ) - 126
17. Kwaryar Bauchi - 114
18. Lagos Island - 111
19. Surulere (Lagos) - 110
20. Ado Odo/Ota (Ogun) - 107
A ranar Asabar, 30 ga watan Mayu, an gwada samfurin mutane 62,583 kuma 10,023 aka samu da cutar.
A cewar rahoton, ba'a samu tabbacin yadda mutane 7,726 suka kamu da cutar ba, hakan na nuna cewa cutar ta yi mumunar yaduwa cikin al'umma.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng