Dalilin da ya sa gwamnati ba ta cire dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi ba da bude makarantu

Dalilin da ya sa gwamnati ba ta cire dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi ba da bude makarantu

A ranar Litinin, 1 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya ta sassauta wasu daga cikin dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar korona a kasar nan.

Hakan ya biyo bayan shawarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba daga kwamitin kar ta kwana na kasa da aka kafa kan cutar korona.

Shugaban kasar ya amince da shawarar kwamitin na sassauta wasu daga cikin dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar a fadin Najeriya.

Shugaban kwamitin wanda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ke jagoranta, ya sanar da cewa sun bai wa shugaban kasar shawara kan matakan da za'a dauka gaba.

Shugaban kasar ya amince a bude wuraren Ibada; Masallatai da Majami'u kadai, da kasuwanni a fadin kasar amma da sharadin za a bi dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta.

Buhari tare da kwamitin kar ta kwana da aka kafa kan cutar korona
Buhari tare da kwamitin kar ta kwana da aka kafa kan cutar korona
Asali: Twitter

Sai dai kwamitin ya ce duk wannan sassauci, za a ci gaba da kiyaye wasu matakai na tsawon makonni hudu masu zuwa kamar yadda shugabar kasar ya ba da lamuni.

Mista Mustapha ya ce har yanzu dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi tana nan kuma za a ci gaba da kiyaye ta, illa iyaka sassauci kan masu jigilar kayan abinci da sauran kayayyakin bukata.

KARANTA KUMA: Dangote, da sauran manyan mutane 7 da suka fi kowa arziki a Afirka

Haka kuma sakataren gwamnatin kasar ya ce an hana duk wani taro da ya haura mutum ashirin in banda a wuraren ibadu ko kuma wuraren aiki.

Gwamnatin tarayya ta kuma tabbatar da cewa, har yanzu makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe a yayin da adadin mutanen da cutar korona ta harba a fadin kasar suka zarta 10,000.

Ya kara da cewa, su na kokarin tabbatar da cewa ma'aikatar ilimi ta tarayya ta samar da ka'idoji da tsare-tsaren bude makarantu cikin aminci ba tare da fargaba ba.

A bangare guda kuma, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa shugaban kasa ya amince a sassauta dokar kullen da aka shimfida a jihar Kano.

Gwamnatin Kano duk da ta amince da umarnin gwamnatin tarayya, ta ce har yanzu dokar kullen tana aiki a jihar a ranakun Litinin, Talata, Alhamis da Asabar kamar yadda aka sani.

Sai dai ta fitar da sabbin kaidoji da dokoki kan yadda za a rika zuwa kasuwanni da wasu wuraren hada-hadar mutane a jihar don rage yaduwar cutar

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Muhammad Garba, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel