Ragargaza 'yan bindiga: Rundunar soji ta kaddamar da sabon atisaye a arewa
Rundunar tsaron hadin guiwa ta Operation Safe Haven da ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya a sassan jihohin Filato, Bauchi da Kaduna ta kaddamar da sabon atisaye mai suna Operation ACCORD don dakile 'yan ta'addan da ka iya tserowa daga yankin arewa maso yamma.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ce ta kaddamar da atisayen Operation Accord din don murkushe 'yan bindiga tare da duk wasu kungiyoyin ta'addanci da suka gallabi yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya na kasar nan.
Kwamandan OPSH, Manjo Janar Chukwuema Okonkwo, yayin kaddamar da atisayen a karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna ya yi jawabi.
Ya ce: "An kirkiro atisayen ne don hadin guiwa da OPSH wajen murkushe ta'addanci kuma zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa 30 ga wata don dakile duk wasu 'yan ta'adda da za su so shigowa yankin."
Janar Okonkwo ya ce za su hada guiwa da Operation Whirl Stroke da kuma dakarun hedkwatarsu da ke Lokoja. Ya ce za su taimaka wajen zakulo 'yan bindigar tare da maboyarsu.
Ya ce: "Ku nemo su tare da batar da su don jama'a su samu damar harkokinsa yadda suka saba.
"Muna bukatar sakamako mai kyau kuma za mu tallafeku."
Ya ce an zabi karamar hukumar Sanga don kaddamar da atisayen ne saboda yawaitar al'amuran 'yan ta'addan a yankin.
KU KARANTA: Ikon Allah: Yadda aka samu shugabannin kasa 2, gwamnoni 4 da ministoci 2 a aji daya
A wani labari na daban, wata kotun laifuka na musamman da ke Ikeja a ranar Litinin ta yankewa wani mutum mai suna Rasak Abiona hukuncin kisa.
Kotun ta zargi Abiona da lakadawa mahaifinsa mai shekaru 62 mugun duka da rodi a yayin da suka samu sa'in'sa a garin Legas.
A hukuncin da aka yanke, Mai shari'a Oluwatoyin Taiwo ya ce, duk da lauyan mai kare kansa ya bada shaidu masu yawa amma kotun ta bincika tare da gano cewa wanda ake zargin ne ya kashe mahaifinsa.
"Wannan mummunan al'amari ne yadda da ya kashe mahaifinsa," Alkalin da ya kama Rasak da laifin kisan kai yace.
"Babu shakka ya so kashe mahaifinsa tunda ya buga mishi rodi a kai.
"Wanda ke kare kansan zai iya gamsar sa mahaifinsa mai shekaru 62 a kan ko mene ne ba tare da buga mishi rodi a kai ba.
"Wannan babban bayani ne a kan abinda fushi da rashin hakuri za su iya kai mutum. A don haka na yanke mishi hukuncin kisa sakamakon kashe mahaifinsa Sunday Abiona," alkalin yace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng