Karin mutum 416 sun harbu da korona a Najeriya, jimilla 10578

Karin mutum 416 sun harbu da korona a Najeriya, jimilla 10578

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 416 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.52 na daren ranar Litinin, 1 ga watan Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 416 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-192

Edo-41

Rivers-33

Kaduna-30

Kwara-23

Nasarawa-18

Borno-17

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sabbin direktoci 6 da Buhari ya nada a NNPC

FCT-14

Oyo-10

Katsina-7

Abia-5

Delta-5

Adamawa-4

Kano-4

Imo-3

Ondo-3

Benue-2

Bauchi-2

Ogun-2

Niger-1

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Litinin 1 ga watan Yunin 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 10578.

An sallami mutum 3122 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 299.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel