Neman tubaraki: Obaseki ya kaiwa Buhari fom dinsa na takarar gwamna a APC

Neman tubaraki: Obaseki ya kaiwa Buhari fom dinsa na takarar gwamna a APC

Gwamnan jihar Edo, Gowin Obaseki, ya gabatar da fom dinsa na sake tsayawa takarar gwamna ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, domin neman tubarakinsa.

A kokarin ceto Obaseki, wasu gwamnonin jam'iyyar APC sun tsinkayi ofishin jam'iyyar a ranar Litinin don yin taron toshe barakar da ke tsakaninsa da Kwamared Adams Oshiomhole, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

An sake shiga wani taron makamancin hakan da shugaban jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu a garin Legas.

Gwamnonin da suka samu halartar taron sun hada da Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredoku, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, Gwamnan jihar Gombe, Mohammed Inuwa.

Sauran sune, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasaki.

Har ila yau, Gwamna Godwin Obaseki ya gaggauta kai ziyara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari fadarsa da ke Aso Villa a Abuja.

Neman tubaraki: Obaseki ya kaiwa Buhari fom dinsa na takarar gwamna a APC
Obaseki ya kaiwa Buhari fom dinsa na takarar gwamna a APC
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ya kai ziyarar ne sakamakon zaben fidda gwani da ke tunkaro jiharsa da kuma rikicin da ke tsakaninsa da Kwamared Adams Oshiomhole a jihar Edo.

An dade ana nuna yatsa tare da musayar maganganu marasa dadi a tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

DUBA WANNAN: Salon nadin mukamanka zai tarwatsa Najeriya - Kanal Dangiwa Umar ya rubutawa Buhari wasika

Rahotanni sun bayyana cewa Obaseki ya shiga damuwa bayan ya fahimci cewar Oshiomhole na shirya ma sa tuggun da zai iya jawo ma sa rasa kujerarsa a zaben fidda dan takarar gwamna na jihar Edo wanda za a yi a cikin watan Yuni.

An samu sabanin ra'ayi a kan hanyar da za a gudanar da zaben fidda dan takara a tsakanin bangaren gwamna Obaseki da bangaren uwar jam'iyyar APC a karkashin jagorancin Oshiomhole.

A yayin da gwamna Obaseki ke son a yi amfani da wakilan jam'iyya domin gudanar da zaben, bangaren Oshiomhole sun kafe a kan a yi kato bayan kato.

Tinubu ya ce ya goyi bayan a gudanar da zaben fidda 'yan takara a cikin jam'iyya domin yin hakan shine tsarin dimokradiyya ta gaskiya da adalci, kuma ta hakan ne kawai dan takara zai gwada karbuwa da farin jininsa a wurin jama'a, wanda hakan shine al'adar siyasa.

Rahotannin sun bayyana cewa Tinubu ya nemi a yi wa gwamnonin da ke kan mulki da sauran ma su sha'awar takara adalci a yayin da ya ke jaddada cewa gudanar da zaben cikin gida zai kara karfafa dimokradiyya da bawa dan takara karfin gwuiwa.

Neman tubaraki: Obaseki ya kaiwa Buhari fom dinsa na takarar gwamna a APC
Obaseki ya kaiwa Buhari fom dinsa na takarar gwamna
Asali: Facebook

Neman tubaraki: Obaseki ya kaiwa Buhari fom dinsa na takarar gwamna a APC
Obaseki ya kaiwa Buhari fom dinsa na takara
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel