Da duminsa: Bayan sassauta dokar ta baci zuwa karfe 10pm-4am, an sanar da ranar bude filayen jirgin sama

Da duminsa: Bayan sassauta dokar ta baci zuwa karfe 10pm-4am, an sanar da ranar bude filayen jirgin sama

Kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19 wato PTF ta sanar da rage awannin dokar ta bacin da aka sa a fadin tarayya zuwa karfe 10 na dare zuwa 4 na Asuba.

Jagoran kwamitin PTF, Dakta Sani Aliyu, ya sanar da hakan ne ranar Litinin a hira da manema labaran da ake gudanarwa a birnin tarayya Abuja.

Yace, "Fari da gobe, Talata, 2 ga Yuni, 2020, za a sassauta dokar hana fita....Dokar ta baci zata cigaba da kasancewa amma an rage lokacin zuwa karfe 10pm zuwa 4am."

"Barin in yi bayanin cewa manufar sa dokar ta bacin ita ce rage cakuduwar mutane, saboda takaita yaduwar cutar."

Hakazalika, gwamnatin tarayya ta bukaci sashen sufurin jiragen sama ta tanadi dokokin da zai taimaka mata wajen fara tashin jiragen cikin gida daga ranar 21 ga Yuni.

Dakta Sani Aliyu, ya bayyana cewa: "Ana bukatar bangaren sufurin sama ta fara shirya ka'idojin barin jirage da tafiye-tafiyen cikin gida su cigaba da aiki fari daga ranar 21 ga Yuni."

"Wajibi ne tashohin jiragen sama su tabbatar da an bada tazara ta hanyar rage adadin fasinjoji da kuma tabbatar da cewa an samar da sinadarin tsaftace hannu da kayan kare kai."

"Hakazalika gwada zafin jikin mutane a hanyoyin shiga da kuma tabbatar da cewa babu cinkoson matafiya ko ma'aikatar tashohon jiragen sama."

Punch ta ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin kulle filayen jirgin sama a watan Maris.

Da duminsa: Bayan sassauta dokar ta baci zuwa karfe 10pm-4am, an sanar da ranar bude filayen jirgin sama
Filin jirgin sama
Asali: Twitter

A bangare guda, Legit.ng Hausa ta kawo rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarar kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan cutar COVID-19 PTF na sassauta dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar.

Shugaban kasan ya amince da bude wuraren Ibada (Masallatai da coci-coci kadai) da kasuwanni a fadin tarayya amma da sharadin za a bi dokokin da hukumar NCDC ta gindaya.

Hakazalika ya amince a sassauta dokar hana fita a jihar Kano da kewaye.

Shugaban kwamitin wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a hirar kwamitin PTF da manema labarai ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel