Yanzu-Yanzu: Buhari ya amince a bude Masallatai, majami'u da kasuwanni a fadin tarayya

Yanzu-Yanzu: Buhari ya amince a bude Masallatai, majami'u da kasuwanni a fadin tarayya

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarar kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan cutar COVID-19 PTF na sassauta dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar.

Shugaban kwamitin wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da cewa an sun gana da shugaba Buhari kuma sun bashi shawara kan matakin da za'a dauka gaba.

Bayan ganawar, Shugaban kasa ya amince da bude wuraren Ibada (Masallatai da Majami'u kadai) da kasuwanni a fadin tarayya amma da sharadin za a bi dokokin da hukumar NCDC ta gindaya.

Yace: "PTF ta mika shawarinta kuma shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a aiwatar da su cikin makonni hudu masu zuwa fari daga ranar 2 zuwa 29 ga watan Yuni, 2020."

"An sassauta dokar hana taruwa a wuraren Ibada bisa ga sharudan da PTF ta gindaya da kuma yardar gwamnatocin jihohi."

"Za'a amince a rika shiga kasuwanni da wuraren tattalin arziki amma da lura saboda takaita yaduwar."

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur a fadin Najeriya zuwa N121.50 ga lita sabanin N125.00 da ake sayarwa yanzu

A bangare guda, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Shugaban kasa ya amince da sassauta dokar hana fita a jihar Kano.

A hirar kwamitin da manema labarai ranar Litinin, 1 ga Yuni, Boss Mustapha, ya sanar da hakan ga daukacin mutan jihar Kano.

Yace: "An sassauta dokar hana fita a jihar Kano."

"Za'a cigaba da taimakawa gwamnatocin jihar wajen tabbatar da cewa su zasu cigaba da gudanar da aikin aiwatar da shawari da dokokin da kwamitin PTF ta gindaya."

"Hukumar NCDC za ta cigaba da baiwa jihohi gudunmuwa ta hanyar basu shawari musamman kananan hukumomin da aiki yayi yawa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel