Zaben Gwamnan Edo da Ondo: Shugabannin jam'iyyu sun shiga ganawar nesa-nesa da INEC

Zaben Gwamnan Edo da Ondo: Shugabannin jam'iyyu sun shiga ganawar nesa-nesa da INEC

- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta gana da shugabannin dukkanin jam'iyyun siyasa na Najeriya sanadiyar zaben gwamnan jihar Edo da Onodo da ke tafe

- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da takwaransa na jam'iyyar adawa ta PDP, Uche Secondus, sun halarci taron

- Hukumar zaben tun a baya ta ba da sanarwar gudanar da zaben a jihohi biyu a watan Satumba na 2020

Yunkurin tumke damarar shirin gudanar da zaben gwamnonin jihar Edo da Ondo, Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta kebance da shugabannin dukkanin jam'iyyu na Najeriya.

An gudanar da wannan zama ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna a ranar Litinin 1 ga watan Yuni, yayin da ake shirin zaben gwamnonin jihohin biyu da za a gudanar a watan Satumba.

Daya daga cikin masu yada rahoton siyasa a gidan talbijin din Channels TV, Seun Okin, shi ne ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a kan shafinsa na Twitter safiyar yau ta Litinin.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Kwamared Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC na kasa da kuma Prince Uche Secondus, shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP, sun halarci taron.

An gudanar da taron ne kan ingatattun hanyoyi da tsare-tsaren INEC da ta tanada domin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali yayin da ake ci gaba da fama da annobar cutar korona.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Gwamna Bello ya shimfida dokar kulle a wani bangare na jihar Kogi

Gabanin wannan taro, INEC ta ba da sanarwa cewa akwai amintattun tsare-tsare da ta tanada wajen gudanar da zaben duk da yadda likafar annobar korona ke ci gaba.

Kwamishinan hukumar, Festus Okoye, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar cikin birnin Abuja tun a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayu.

Mista Okoye ya ce duk da dagula al'amura da annobar korona ta yi wa jihohin kasar nan, zaben zai gudana kamar yadda aka tsara.

A baya dai jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar APC ta fidda jadawalin gudanar da zaben fidda gwanin takara na gwamnonin jihohin Ondo da Edo.

Jam'iyyar mai ci a kasar ta sanya ranar Litinin 22 ga Yuni a matsayin ranar gudanar da zaben fidda gwanin takarar gwamnan jihar Edo, sai kuma jihar Ondo, da aka sanya wa ranar Litinin, 20 ga watan Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng