Coronavirus: Gwamna Bello ya shimfida dokar kulle a wani bangare na jihar Kogi

Coronavirus: Gwamna Bello ya shimfida dokar kulle a wani bangare na jihar Kogi

Daga karshe, uwar bari ta sanya gwamnan jihar Yahaya Bello na jihar Kogi, ya shimfida dokar kulle a wani bangare na jihar biyo bayan samun bullar cutar korona.

Gwamnan ya yi riko da gargadin da Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa a kasar NCDC ta yi, inda cikin gaggawa ya shimfida dokar kulle a gaba daya karamar hukumar Kabba-Bunu.

Gwamna Bello ya yanke hukuncin da ya zartar a kan karamar hukumar Kabba-Bunu cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin 1 ga watan Yuni.

Sanarwar da babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin Kogi, Onugwo Muhammed ya gabatar wa da jaridar Legit.ng, ya bayyana cewa ko shige-da-fice a tsakanin gida-zuwa-gida ya haramta.

Gwamnan jihar Kogi; Yahaya Bello
Gwamnan jihar Kogi; Yahaya Bello
Asali: UGC

Mai magana da yawun gwamnatin ya ce akwai mahukunta da aka dorawa nauyin ci gaba da lalube da farautar mutanen da suka yi cudanya da wadanda suka fara kamuwa da cutar a jihar.

KARANTA KUMA: Zaben Gwamnan Edo da Ondo: Shugabannin jam'iyyu sun shiga ganawar nesa-nesa da INEC

Haka kuma, gwamnatin cikin gaggawa ta umarci ma'aikatan lafiya da suka duba marasa lafiyan da cutar ta harba da su killace kawunansu domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Gwamnatin jihar ta gargadi al'umma da su tabbatar sun kiyaye dokar kullen da kuma matakan da NCDC ta shimfida.

A baya jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin Kogi ta gano tuggun da ake kullawa na neman ta dole sai an shigo da kwayoyin cutar korona cikin jihar ta kowace irin haramtacciyar hanya.

Gwamnatin jihar ta ce wannan yana daya daga cikin makarkashiyar da ake kulla wa na neman sai an tursasawa kowace jiha a fadin Najeriya samun bullar cutar korona.

Ta yi zargin cewa "a baya-bayan nan akwai miyagun da ke ci gaba da matsin lamba ta lallai sai an lalubo masu cutar tare da kaddamar da bullar ta a jihar."

Kwanaki kadan da suka gabata ne jihar Kogi ta shiga sahun jihohin da cutar ta bulla yayin da aka samu mutum biyu dauke da kwayoyin cutar kmaar yadda alkaluman NCDC suka nuna.

Sai dai sa'o'i kadan da ba da wannan sanarwa ta NCDC, gwamnatin jihar ta yi watsi da rahoton bullar cutar a cikin jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Haruna Audu, ya ce ba za su amince da kirkire-kirkiren labarai da cibiyar NCDC ta yada a kansu ba, inda ya nanata matsayin gwamnatin jihar Kogin da cewa har yanzu babu cutar korona a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel