Zaben Edo da Ondo: Gwamnonin APC 9 sun gana da Tinubu

Zaben Edo da Ondo: Gwamnonin APC 9 sun gana da Tinubu

- Gwamnoni tara karkashin jagorancin Atiku Bagudu na Kebbi, sun gana da jigon jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, domin neman goyon baya a kan takwarorinsu na Ondo da Edo

- Amma abin takaici ga masu goyon bayan Gwamna Godwin Obaseki, APC na iya ci gaba da shirinta na aiwatar da zaben kai tsaye yayin fidda gwanin takara a jihar Edo

- An tabbatar da cewa gwamnonin suna son jam'iyyar ta sauya tsarin zaben amma Tinubu ya nace cewa dole ne a yi adalci kuma a gudanar da zaben fidda gwanin yadda aka saba

A yanzu rikicin jam'iyyar APC ya sauya wani salo mai karfin gaske, yayin da gwamnoni tara suka gana da Asiwaju Bola Tinubu, dangane da zaben gwamna da ke tafe a jihohin Edo da Ondo.

Gwamnonin karkashin kungiyar ci gaban gwamnoni ta PGF, wanda gwamnan jihar Kebbi ya jagoranta, sun gana ne a gidan gwamnatinsa da ke unguwar Marina a jihar Legas.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, gwamnonin sun hadar da Godwin Obaseki na jihar Edo, Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, Simon Lalong na Filato da Mai Mala Buni na jihar Yobe.

Sauran sun hadar da Adegboyega Oyetola na jihar Osun, Abdullahi Ganduje na Kano, Abubakar Bello na Neja da kuma Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos.

Daga cikin muhimman abubuwa da suka tattauna, gwamnonin sun nemi Tinubu, wato kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, da ya tabbatar masu da goyon baya a kan gwamnan Edo.

Gwamnonin APC 9 yayin ganawa da Tinubu
Gwamnonin APC 9 yayin ganawa da Tinubu
Asali: Twitter

Gwamnonin sun nemi Tinubu ya jaddada masu goyon bayan sa a kan gwamna Obaseki yayin da zaben jihar sa zai wakana a watan Satumba.

Tun a baya dai jam'iyar APC ta ba da sanarwa gudanar da tsarin zabe na kai tsaye yayin fidda gwanin takara.

KARANTA KUMA: Yankin Kudu maso Yamma ya fi ko ina samun mukamai a gwamnatin Buhari - Boss Mustapha

Sai dai wannan tsari ana ganin zai haddasa tangarda a nasarar gwamna Obaseki, saboda zaman doya da manja da ke tsakaninsa da tsohon ubangidansa na siyasa.

Sai dai Tinubu ya nace a kan cewa dole ne a bi tsari da kuma ka'idojin da shugabannin jam'iyyar ta APC suka shimfida, wajen an gudanar da zaben kai tsaye yayin fitar da gwanin takara.

A zaman da aka shafe tsawon sa'o'i biyu, Tinubu ya tunasar da cewa, tsarin zabe na kai tsaye aka gudanar wajen tsayar da gwamnan jihar Legas da na Osun a matsayin 'yan takara a jihohinsu.

Tinubu wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Legas, ya jaddada yakininsa a kan tabbatar da gaskiya da kuma adalci, inda ya ce zaben kai tsaye shi ne zai tabbatar da dimokuradiya a kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel