Dalilin da ya sa Buhari ya kasa yi wa 'yan Najeriya jawabi a ranar 29 ga watan Mayu - PDP

Dalilin da ya sa Buhari ya kasa yi wa 'yan Najeriya jawabi a ranar 29 ga watan Mayu - PDP

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP, ta ba da shaidar dalilin da ya sanya shugaba Muhammadu Buhari, bai yi wa 'yan Najeriya jawabi ba a ranar 29 ga watan Mayu.

Jam'iyyar ta ce akwai gazawa a gwamnatinsa ta rashin tsinana wani abu mai muhimmanci da zai yi tasiri a kan 'yan Najeriya cikin tsawon shekaru biyar da ta shafe a kan gado na mulki.

Ta ce wannan shi ne dalilin da ya hana shugaba Buhari fuskantar 'yan Najeriya da jawabai a ranar 29 ga watan Mayu, duk da ta kasance tsohuwar ranar dimokuradiya a kasar.

Gabanin shekarar da ta gabata, an saba samun hutu tare da yin shagali a ranar 29 ga watan Mayu ta kowace shekara, domin tunawa da ranar da mulkin kasar ya koma hannun farar hula.

A shekarar da ta gabata ne shugaba Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta sauya wannan rana zuwa ranar 12 ga watan Yuni.

Sabanin yadda aka saba a kowace shekara, shugabannin Najeriya su kan gabatar da jawabai a wannan rana, inda a bana babu ko uffan da ya fito daga bakin shugaba Buhari.

Dalilin haka ya sanya jam'iyyar PDP ta yi wa shugaban kasar wankin babban bargo tare da ba da shaidar abin da ta fahimta dangane da shiru din da shugaban kasar ya yi.

Buhari da kakakin jam'iyyar PDP na kasa; Kola Ologbondiyan
Buhari da kakakin jam'iyyar PDP na kasa; Kola Ologbondiyan
Asali: UGC

Cikin sanarwar da kakakin jam'iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Lahadi, ya ce ganin babu abin da shugaba Buhari zai iya fada wa 'yan Najeriya ya sa ya ja bakinsa ya yi shiru.

Ya ce gudun kada Buhari ya fito ya shirgawa 'yan Najeriya karya da kuma kunyar fuskantar saboda bai tsinana komai, ta sanya ya ki fitowa ya fuskance su da jawabai.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta amince da sauya ranar Dimokuradiya a Najeriya

“Tabbas, mai yiwuwa shugaba Buhari ba ya son fuskantar ‘yan Najeriya da wani uzuri na rashin gaskiya wanda ya lalata tattalin arzikinmu mai karfi; saboda gazawar tabbatar da tsaron kasarmu, gazawa wajen dakile cin hanci da rashawa a cikin gwamnatinsa da kuma cefanar da kasar ga manyan kasashe wajen rancen kudi."

"Babu wasu kalamai masu gamsarwa da shugaban kasar zai yi wa 'yan Najeriya fiye da miliyan 40 da suka rasa ayyukansu, sakamakon gazawar gwamnatinsa wajen inganta tattalin arzikin kasar."

"Bugu da kari, shugaban Buhari ya gaza bayar da dalilai na karyewar darajar Naira da kuma raguwar kudaden kasar na ajiya a kasashen ketare."

"Haka kuma gwamnatinsa ta gaza rage farashin mai a kasar duk da hauhawar da farashinsa ya yi a kasuwar duniya."

"Shugaba Buhari yana fuskantar kalubalai na rashin gano mafita dangane da kashe-kashen da ake yi a Sakkwato, Katsina, Kaduna, Kogi, Zamfara, da sauran jihohin da 'yan fashi da masu garkuwa da mutane da kuma masu tayar da kayar baya duk da ikirarin da gwamnatinsa ta yi na cewa an durkusar da masu kai hare-haren."

"A daidai wannan gaba kuma, shugaba Buhari ya gaza samun nasara dangane da yadda gwamnatinsa ta APC ta ke tunkarar lamarin annobar cutar korona, wanda a halin yanzu ake zargin cin hanci da rashawa da kuma siyasa sun mamaye lamarin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel