Ahmed Musa, kyaftin din Super Eagles, ya bayyana motocinsa masu tsada a shafukan sada zumunta

Ahmed Musa, kyaftin din Super Eagles, ya bayyana motocinsa masu tsada a shafukan sada zumunta

- A yanzu Ahmed Musa ya kasance daya daga cikin 'yan wasan Super Eagles da suka yi fice a duniya

- Dan wasan ya taka leda a Ingila, Netherlands, Russia kafin ya koma kungiyar Al Nassr ta Saudiya

- Shi kadai ne dan Najeriya daya tilo da a tarihi ya zira kayatattun kwallaye hudu a gasar cin kofin duniya

- Ya bayyana dukiyar da ta ke cikin garejinsa mai dauke da motoci na alfarma yayin da yake wasan kwallon tebur.

Ahmed Musa, kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar Najeriya da ake kira Super Eagles, ya kasance dan wasan Najeriyar da ya fi kowa fice a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan gaba da ke taka leda a kungiyar kwallo ta Al Nassr, ya zira kyawawan kwallaye hudu a gasar cin kofin duniya da aka buga a shekarar 2014 da kuma 2018.

Sai koda yake, nasarorinsa ba su takaita kadai ba a filin kwallo, wajen jefa kwallo a koma wanda hakan yana taimakawa kungiyoyinsa daban-daban su lashe gasa.

Tsohon dan wasan na kungiyar Leicester City, cikin salo ya sanya hoton garejin motocinsa a kafafen sada zumunta yayin da ya ke wasan kwallon tebur tare da wani.

Ahmed Musa wanda ya taka leda a kungiyar CSKA Moscow daga shekarar 2012 zuwa 2016, ya na da motoci na alfarma da aka kera a shekarar 2019 wanda darajarsu ta kai kusan naira miliyan 200.

Daga cikin jerin motocinsa akwai, Mercedes Benz G-Wagon wanda aka kiyasin kudinta ya kai N120m, Range Rover Velar, wadda ta kai kimanin N40m da kuma Porsche Macan wanda farashinta ya doshi N30m.

Haifaffen jihar Filato, yana daga cikin 'yan wasan Super Eagles da suka lashe lambar tagulla a gasar cin kofin kasashen Afirka ta shekarar 2019 da aka buga a kasar Masar a bara.

Wannan nasara da suka samu a bara ta faru ne shekaru shida bayan da tawagarsu ta lashe gasar cin kofin kasashen Afrika (AFCON) da aka buga a kasar Afrika ta Kudu.

KARANTA KUMA: Babu wani abu mai muhimmanci da Buhari ya tsinana cikin shekaru 5 - PDP

Dan wasan mai shekaru 27 da haihuwa, an nada shi kyaftin din tawagar Super Eagles bayan ficewar tsohon dan wasan tsakiya John Obi Mikel daga kungiyar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kyaftin din na Super Eagles ya nisantar da kansa daga labarin da yake danganta shi da barin kungiyar sa ta Al Nassr da ke Saudiya a wannan bazarar.

An ci gaba dai da danganta dan wasan na gaba da komawa nahiyyar Turai, yayin da kungiyar Fenerbahce ta nuna ra'ayi tare da ci gaba da zawarcin fitaccen dan wasan na Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: