Salon nadin mukamanka zai tarwatsa Najeriya - Kanal Umar ya rubutawa Buhari wasika

Salon nadin mukamanka zai tarwatsa Najeriya - Kanal Umar ya rubutawa Buhari wasika

Tsohon gwamnan jihar Kaduna a mulkin soji, Kanal Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya), ya rubuta budaddiyyar wasika zuwa ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tare da gargadinsa a kan cewa salon nadin mukamansa zai iya rusa Najeriya.

A cikin wasikarsa mai taken: 'Shugaban kasa; ka zama na kowa da kowa', Umar ya ce salon nadin mukaman gwamnatin Buhari, wanda ya karkata zuwa bangare guda, zai iya jefa kasa a cikin rikici.

Ya zargi shugaban kasa da fifita wani bangare na kasa a kan sauran a yayin nadin sabbin mukamai a gwamnatinsa.

Kanal Umar ya rubuta wasikar ne a matsayin furucinsa a yayin da ake murnar cikar Buhari shekaru biyar a kan kujerar shugaban kasa

Wasikar, mai dauke da kwanan watan 31 ga watan Mayu, ta ce "duk ma su yi wa Najeriya fatan alheri ya zama dole su fada ma ka gaskiya tare da gargadinka a kan hatsarin da ke tattare da jirgewar gwamnatin tarayya a bangare guda yayin nada mukamai.

Salon nadin mukamanka zai tarwatsa Najeriya - Kanal Umar ya rubutawa Buhari wasika
Buhari da shugabannin runduonin tsaro na ksa
Asali: Facebook

"Gwamnatinka ta cigaba da yin kuskure na fifita bangare guda a kan sauran bangarorin kasar nan.

"Babu inda wannan son kai ya fito kuru - kuru kamar a nadin shugabannin hukumomi da rundunonin tsaro na kasa.

DUBA WANNAN: Hotunan sashen filin jirgin sama na Kano da gwamnatin Buhari ta zamanantar

"Mai girma shugaban kasa, babu wasu kalmomi ma su dadi da zan iya amfani da su wajen isar da wannan sako gareka, bawa wani bangare fifiko zai saka fushi da kiyayya a zukatun jama'ar sauran bangarorin, lamarin da zai haifar da fitina da rusa kasa baki daya.

"Idan za ka iya tunawa na taba rokon ka karawa tsohon alkalan alkalai na kasa (CJN), Walter Onnoghen, lokaci a yayin da ya rage saura 'yan kwanaki ya kammala wa'adinsa, amma sai ka zabi dan arewa Musulmi.

"Mataimakinka, Farfesa Yemo Osinbajo, ya hana gwamnatinka jin kunya ta hanyar aika sunan Onnoghen zuwa majalisar dattijai a lokacin da ya ke mukaddashin shugaban kasa.

"An sauke Onnoghen daga mukamin CJN watanni kadan bayan nada shi tare da maye gurbinsa Jastis Muhammed, Musulmi dan arewa, " a cewar kanal Umar.

Kanal Umar ya ce haka shugaba Buhari ya yi ta jan kafa wajen nada jastis Monica Dongban Mensem a matsayin shugabar alkalan kotun daukaka kara saboda kasancewarta kirista daga yankin arewa.

A cewarsa, da kyar shugaba Buhari ya amince da nadinta bayan an rasa hanyar da za a bi domin a zagayeta, a bayar da mukamin ga mataimakinta, Musulmi dan arewa.

Tsohon sojan ya bukaci shugaba Buhari ya sake salo wajen nada mukamai domin gudun illar da hakan zai iya haifarwa ga kasa nan gaba.

Shugaba Buhari ya dade ya na shan suka a kan kin sauya shugabannin rundunonin sojojin Najeriya duk da kasancewar wa'adinsu na barin aiki ya dade da shudewa.

Har yanzu shugaba Buhari bai sauyasu ba kuma bai bayyana dalilin cigaba da aiki tare da su ba, lamarin da ya sa wasu ke cigaba da guna - gunin cewa ya zabi cigaba da aiki tare da su ne saboda dalilai na bangaranci da nuna son kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel