Nasara daga Allah: Babban asirin Boko Haram ya tonu a Borno - DHQ

Nasara daga Allah: Babban asirin Boko Haram ya tonu a Borno - DHQ

Hedkwatar tsaro ta kasa da ke Abuja, ta ce rundunar sojin Operation Lafiya Dole ta gano cewa mayakan Boko Haram da ke yankin Isari a karamar hukumar Gamboru Ngala sun haka ramuka.

A ranar Litinin, rundunar sojin ta tabbatar da cewa ta bankado ramuka da aka haka da kyau a kauyukan Gulwa, Diime, Musiri, Wuri Bari, Mada, Sangaya, Jarawa, Mutu, Isari da Mudu a karamar hukumar.

A wata takarda da fannin yada labaran dakarun ta fitar, ta ce wasu daga cikin manyan mayakan Boko Haram din sun mika kansu kuma an karbesu, The Punch ta ruwaito.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar Enenche, ya ce, "A yayin da rundunar sojin Najeriya ke gab da samun nasarar karar da mayakan Boko Haram, wasu daga cikin 'yan ta'addan na mika wuya ga dakarun bayan tarwatsa maboyarsu da gidajensu.

"Dakarun da ke sansani na 11 a Gamboru sun gano wata maboyar 'yan ta'addan inda suka haka ramuka. Sun damke 'yan ta'adda uku tare da samun bindiga kirar AK 47 daya a tare dasu.

"A ranar 29 ga watan Mayun 2020, wani mayakin ta'addancin mai suna Muhammadu Abubakar wanda aka fi sani da Babagana, ya mika kansa ga bataliya ta 242 da ke Monguno, jihar Borno.

"Binciken farko ya bayyana cewa, matashin mai shekaru 19 ya shiga kungiyar ta'addancin kusan shekara daya kenan a Shaharam kuma ya taka rawar gani a harin Tumbun Shaje.

"Babagana ya yi kira ga rundunarsa da su mika wuya ga dakarun. Adamu Yahaya, abokin ta'addancin Babagana ya mika wuya ga bataliya ta 242."

KU KARANTA: Cashewar matan aure a gaban mazansu: Mawaki Hamisu Breaker ya yi karin haske

Nasara daga Allah: Babban asirin Boko Haram ya tonu a Borno - DHQ
Nasara daga Allah: Babban asirin Boko Haram ya tonu a Borno - DHQ. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

A wani labari na daban, rundunar tsaron hadin guiwa ta Operation Safe Haven da ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya a sassan jihohin Filato, Bauchi da Kaduna ta kaddamar da sabon atisaye mai suna Operation ACCORD don dakile 'yan ta'addan da ka iya tserowa daga yankin arewa maso yamma.

Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ce ta kaddamar da atisayen Operation Accord din don murkushe 'yan bindiga tare da duk wasu kungiyoyin ta'addanci da suka gallabi yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya na kasar nan.

Kwamandan OPSH, Manjo Janar Chukwuema Okonkwo, yayin kaddamar da atisayen a karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna ya yi jawabi.

Ya ce: "An kirkiro atisayen ne don hadin guiwa da OPSH wajen murkushe ta'addanci kuma zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa 30 ga wata don dakile duk wasu 'yan ta'adda da za su so shigowa yankin."

Janar Okonkwo ya ce za su hada guiwa da Operation Whirl Stroke da kuma dakarun hedkwatarsu da ke Lokoja. Ya ce za su taimaka wajen zakulo 'yan bindigar tare da maboyarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel