Gwamna Bauchi ya bayyana wani babban al'amari da ke faruwa da shi

Gwamna Bauchi ya bayyana wani babban al'amari da ke faruwa da shi

Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, ya ce yana fama da mummunan kalubale da adawa tun bayan da ya hau kujerar shugabancin jihar.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Asabar bayan cikarsa shekara daya a kan karagar mulkin jihar, Mohammed ya ce yana fama da wasu mutane da suka hade masa kai duk da ya taba aiki tare da su kafin ya zama gwamna.

"Muna iyakar kokarinmu wajen aiki ba don a jinjina mana ba, muna yi ne don sauke nauyin da ke kanmu," Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito.

"Kwamishinoni na na korafi amma dole ne mu sadaukar da wasu abubuwan don nuna godiya ga Allah da kuma jama'ar jihar Bauchi da suka zabe mu.

"Ina fama da kalubale amma kuma jama'ar sun yarda dani. Ina fama da adawa don ko a yanzu akwai wadanda suka hade min kai.

"Wasu jama'a ne suka hade min kai duk da mun yi aiki tare kafin kai wa ta wannan matsayi," gwamnan yace.

Mohammed ya ce bashi da ubangida ko wani wanda yake bashi umarni. Don haka aikinsa yake na sauke nauyin da jama'a suka dora masa.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, da yawa daga cikin ayyukan da gwamnatinsa ta fara an yi su ne da naira biliyan 11 da hukumar yaki da rashawa ta kwato sannan ta mika musu.

Gwamna Bauchi ya bayyana wani babban al'amari da ke faruwa da shi
Gwamna Bauchi ya bayyana wani babban al'amari da ke faruwa da shi. Hoto daga Channels TV
Asali: Facebook

KU KARANTA: An tsinta gawar tsohon kwamishinan da 'yan bindiga suka sace a daji

A wani labari na daban, dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, jihar Ogun, ya sallami ma'aikata sakamakon matsin rayuwar da annobar Covid-19 ta janyo.

Shugaban bangaren kula na dakin karatun, Olanike Ogunleye, a wata wasika da jaridar The Nation ta bayyana, ta ce ci gaban ya faru ne sakamakon illar da annobar korona ta yi wa wurin.

Hukumar dakin karatun ta bayyana cewa, annobar ta sa ba za su iya rike yawan ma'aikatansu ba kamar yadda suka yi a da.

Kamar yadda wani bangare na wasikar ya bayyana: "Kamar yadda aka sani, annobar korona ta yi babbar illa ga kasuwancinmu.

"Wannan ne yasa kasuwacinmu yayi kasa. Saboda haka, cike da damuwa muke sanar da ku cewa mun sallame ku daga aiki.

"Ana bukatar ku mila dukkan kadarorin kamfani da ke hannunku yayin da zaku karba takarda tare da kudin sallama."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel