Jerin sunayen sabbin direktoci 6 da Buhari ya nada a NNPC

Jerin sunayen sabbin direktoci 6 da Buhari ya nada a NNPC

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin direktocin hukumar man fetur ta Najeriya, (NNPC).

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis.

Shugaban kasar ya sake zaben sabbin direktocin hukumar ne bayan karewar waadin tsaffin mambobin da aka nada a shekarar 2016.

An zabo direktocin ne daga yankuna shida na kasar nan.

Ga jerin sunayensu a kasa.

1. Mohammed Lawal (Arewa maso yamma)

2. Tajudeen Umar (Arewa maso gabas)

3. Adamu Mahmood Attah (Arewa maso tsakiya)

DUBA WANNAN: Buhari ya fi amincewa da mata fiye da maza - Garba Shehu

4. Senator Magnus Abe (Kudu maso Kudu)

5. Dr Stephen Dike (Kudu maso gabas) da

6. Chief Pius Akinyelure (Kudu maso yamma)

Direktocin da aka nada za suyi aiki ne na tsawon shekaru uku.

A wani rahoton, mun kawo muku labarin rasuwar shugaban kamfanin man fetur ta Najeriya NNPC, Dr Maikanti Kachalla Baru da ya rasu a daren ranar Jumaa.

Shugaban kamfanin ta NNPC mai ci yanzu, Mele Kyari, ya sanar da labarin rasuwarsa a shafinsa na Twitter da safiyar nan inda ya ce marigayin ya rasu ne a daren jiya.

Yace: "Dan'uwana, abokina kuma malamina, Dr Maikanti Kachalla Baru, tsohon shugaban NNPC, ya rasu a daren jiya."

"Ya kasance mutum mai kyawawan halayen da dabi'a. Allah ya gafarta masa kura-kuransa kuma ya yi masa rahama."

A bangarensa, Shugaba Muhammadu Buhari shima ya yi sakon taaziyar rasuwar marigayi MaiKanti Baru.

Ya yi adduar Allah ya jikansa ya kuma gafarta masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel