Yanzu-yanzu: Dan uwan Buhari, Ibrahim Dauda ya rasu

Yanzu-yanzu: Dan uwan Buhari, Ibrahim Dauda ya rasu

Allah ya yi wa dan uwan Shugaba Muhammadu Buhari, Ibrahim Dauda rasuwa.

Ibrahim Dauda ya rasu ne a Daura, jihar Katsina bayan ya dade yana fama da rashin lafiya.

A sakon taaziyar Shugaba Buhari da mai magana da yawunsa kasa Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ya ce rasuwar Dauda babban rashi ne ga mutanen Daura.

Shugaban kasar ya ce, "Na yi matukar alhinin rashin wani dan uwa na, mutumin kirki da ya nuna karamci da gaskiya a dukkan harkokinsa."

DUBA WANNAN: Buhari ya fi amincewa da mata fiye da maza - Garba Shehu

Ya yi adduar Allah ya jikan marigayin kuma ya saka masa da gidan aljanna.

Marigayin ya rasu ya bayar yaya masu yawa cikinsu har da Dauda Ibrahim, babban maaikaci a gidan gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel