COVID-19: Dakin karatun Olusegun Obasanjo ya sallami ma'aikata

COVID-19: Dakin karatun Olusegun Obasanjo ya sallami ma'aikata

- Dakin karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, jihar Ogun ta sallami ma'aikata masu tarin yawa

- Kamar yadda hukumar dakin karatun ta bayyana, matsin da kasar nan ta shiga na tattalin arziki sakamakon annobar korona ne ya jawo hakan

- An bukaci ma'aikatan da su mika dukkan kadarorin da ke hannunsu wanda mallakin hukumar ne

Dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, jihar Ogun, ya sallami ma'aikata sakamakon matsin rayuwar da annobar Covid-19 ta janyo.

Shugaban bangaren kula na dakin karatun, Olanike Ogunleye, a wata wasika da jaridar The Nation ta bayyana, ta ce ci gaban ya faru ne sakamakon illar da annobar korona ta yi wa wurin.

Hukumar dakin karatun ta bayyana cewa, annobar ta sa ba za su iya rike yawan ma'aikatansu ba kamar yadda suka yi a da.

Kamar yadda wani bangare na wasikar ya bayyana: "Kamar yadda aka sani, annobar korona ta yi babbar illa ga kasuwancinmu.

"Wannan ne yasa kasuwacinmu yayi kasa. Saboda haka, cike da damuwa muke sanar da ku cewa mun sallame ku daga aiki.

"Ana bukatar ku mila dukkan kadarorin kamfani da ke hannunku yayin da zaku karba takarda tare da kudin sallama."

An gano cewa, an mika wasikar ga ma'aikatan da abun ya shafa a ranar Juma'a amma tana dauke da kwanan watan 25 ga watan Mayu.

COVID-19: Dakin karatun Olusegun Obasanjo ya sallami ma'aikata
COVID-19: Dakin karatun Olusegun Obasanjo ya sallami ma'aikata. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kada ku bar 'yan bindigar Zamfara su gangaro Kaduna - El-Rufai ya roki soji

A wani labari na daban, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya sanar da dage dokar takaita zirga-zirga ta wucin-gadi a kowacce ranar Juma'a.

Masari ya dage dokar hana tarukan addinai da kuma yawo tsakanin kananan hukumomin jihar.

Gwamnan jihar Katsina ya ce, wannan hukuncin ya biyo bayan kokarinsu na ganin cewa Musulmi da Kiristan jihar sun yi al'amuransu na addini a kowacce ranar Juma'a tare da samo abubuwan bukata a kasuwanni.

Ya ce dole ne a samar da sinadarin tsaftace hannu a kowanne wurin bauta don amfanin masu bautar kafin shigarsu farfajiyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel