An tsinta gawar tsohon kwamishinan da 'yan bindiga suka sace a daji

An tsinta gawar tsohon kwamishinan da 'yan bindiga suka sace a daji

Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta samu gawar tsohon kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Presley Ediagbonya a daji.

Wasu 'yan bindiga ne suka sace Ediagbonya a gonarsa da ke kauyen Utese, karamar hukumar Ovia ta arewa maso gabas a ranar 16 ga watan Mayun 2020.

A wata takarda da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Chidi Nwabuzor ya fitar, ya ce an tsinta gawar tsohon kwamishinan a wani daji da manoma ke aiki a kusa da iyakar jihar Ondo.

"Rundunar 'yan sandan jihar Edo na sanar da cewa ta tsinta gawar Ediagbonya a ranar 29 ga watan Mayun 2020.

"P.E Ediagbonya tsohon kwamishinan matasa da wasanni na jihar Edo. Wasu manoma ne suka tsincesa a dajin da ke da iyaka da jihar Ondo a kauyen Utese," yace.

Ya ce manoman sun gaggauta komawa cikin kauyen inda suka sanar da labarin ga jami'an 'yan sanda.

Ya ce, "Da gaggawa DPO ya tura mutanensa inda suka tuntubi masana kiwon lafiya na jami'ar Igbinedion sannan suka tunkari dajin tare da iyalan mamacin da manoman."

Kamar yadda yace, tuni iyalan mamacin suka gano gawarsa sannan cike da kwarewa aka dauke gawar don kai ta ma'adanar gawawwaki da ke asibitin koyarwa na jami'ar Igbinedion don bincike.

Kwanaki biyu kenan da hankula suka tashi bayan sace tsohon kwamishinan da wasu 'yan bindigar suka yi.

An tsinta gawar tsohon kwamishinan da 'yan bindiga suka sace a daji
An tsinta gawar tsohon kwamishinan da 'yan bindiga suka sace a daji. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kada ku bar 'yan bindigar Zamfara su gangaro Kaduna - El-Rufai ya roki soji

A wani labari na daban, rayuka 15 ne suka salwanta a kananan hukumomin Faskari da Sabuwa a wani mummunan harin da 'yan bindiga suka kai yankin ranar Alhamis.

'Yan bindigar sun kai harin Unguwar Gizo, Maigora, Mai ruwa da Sabon Layin Galadima da ke karamar hukumar Faskari ta jihar.

Sun hari kauyen Machika da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina. Ganau ba jiyau ba, sun ce 'yan bindigar sun kai harin ne a tsakar daren Alhamis inda suka dinga barna har zuwa safiyar Juma'a.

An gano cewa, mazauna yankin sun yi yunkurin mayar da martani amma hakan sai ya jawo rashin rayuka. Mutum 15 suka rasa rayukansu inda 'yan bindigar suka yi awon gaba da Shanu masu tarin yawa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, yayin tsokaci a kan yawan wadanda suka rasa rayukan su, ya ce mutum goma sha uku ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel