Cutar korona ta hallaka babban Limami, Sheikh Ahmad Abubakar

Cutar korona ta hallaka babban Limami, Sheikh Ahmad Abubakar

Iyalan babban limamin garin Kabba, Sheikh Ahmad Abubakar Ejibunu, sun tabbatar da cewa ya mutu ne sakamakon kamuwa da kwayar cutar korona.

An dade ana cacar baki da musayar yawu a tsakanin hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa (NCDC) da gwamnatin Kogi a kan bullar annobar korona a jihar.

A yayin da hukumar NCDC ta bayyana cewa an samu mutane biyu da ke dauke da kwayar cutar korona a jihar, gwamnatin Kogi ta kafe a kan cewa annobar ba ta bullar jihar ba har yanzu.

Amma iyalan Sheikh Ejibunu sun fadawa gwamnatin jihar Kogi cewa "su daina musun cewa akwai annobar a jihar".

Tai Ejibunu, daya daga cikin iyalin marigayin, ya ce babban limamin ya nuna alamu irin na masu fama cutar korona tun kafin sakamakon gwajinsa ya tabbatar da cewa ya na dauke da kwayar cutar.

"Hankalinmu ya kai kan wata mahawara da musayar yawun da ake yi a kan mutumin da annobar cutar korona ta hallaka a garin Kabba.

"Amadadin iyali da dangin Ejibunu, ina mai sanar da cewa marigayi Sheikh Ahmad Abubakar Ejibunu, babban limamin garin Kabba, ya kwanta rashin lafiya a asibitin kwararru da ke Kabba bayan ya kamu da wata mura mai zafi.

"Mun mayar da shi zuwa babban asibitin gwamnatin tarayya (FMC) da ke garin Lokoja bayan al'amura sun kara zafafa.

"Daga FMC Lokoja aka bamu shawarar mu mayar da shi babban asibitin kasa da ke Abuja, inda a nan ne jami'an NCDC su ka gwada shi kuma su ka tabbatar da cewa ya na dauke da kwayar cutar korona.

"Sakamakon gwajin da aka yi wa dansa da ke tare da shi ya nuna cewa shi bai kamu da kwayar cutar ba.

Cutar korona ta hallaka babban Limami, Sheikh Ahmad Abubakar
Cutar korona ta hallaka babban Limami, Sheikh Ahmad Abubakar
Asali: UGC

"Ya kamata mu fito mu yi magana a kan lamarin, amma ba ma jin dadin yadda ake musayar yawu da cacar baki a tsakanin NCDC da gwamnatin jihar Kogi.

"Mun damu da lafiyar sauran jama'a, a saboda haka ya kamata mu sanar da cewa annobar cutar korona ta shigo cikin al'ummarmu da jiharmu.

DUBA WANNAN: Barden yakin kungiyar Boko Haram, Saad Karami, ya mika wuya ga rundunar soji

"A saboda haka, babu wata bukatar a boye gaskiya, gwamnatin jihar Kogi ta daina musanta abinda ya riga ya bayyana.

"Ya na da kyau mu sanar da jama'a cewa marigayi Sheikh Ejinubu bai yi bulaguro zuwa ko ina ba gabanin ya fara rashin lafiya. Ya kamu da kwayar cutar ne yayin mu'amala da mutane a garin Kabba.

"Mu na shawartar jama'a su kasance ma su biyayya ga dokokin hukumar NCDC domin kiyaye kansu.

"Mu na bawa gwamnatin jihar Kogi da hukumar NCDC hadin kai domin dakile yaduwar kwayar cutar.

"Yanzu haka an fara gwada mambobin iyalan marigayi Sheikh Ejibunu.

"Mu na bukatar sauran jama'a su bawa hukuma hadin kai tare da bayar da muhimman bayanai da za su taimaka wajen shawo kan yaduwar cutar a jihar Kogi.

"Allah ya kare garinmu da jama'arsa da sauran jama'ar jihar Kogi daga wannan annoba," a cewar jawabin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel