COVID-19: Sabbin mutum 387 sun kamu a Najeriya, Jigawa 24, Kaduna 11

COVID-19: Sabbin mutum 387 sun kamu a Najeriya, Jigawa 24, Kaduna 11

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 387 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.46 na daren ranar Jumaa, 29 ga watan Mayun na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 387 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-254

FCT-29

Jigawa-24

Edo-22

Oyo-15

Rivers-14

Kaduna-11

DUBA WANNAN: Birai sun gudu da kayan gwajin COVID-19 bayan kai wa ma'aikacin lafiya hari

Borno-6

Kano-3

Plateau-2

Yobe-2

Gombe-2

Bauchi-2

Ondo-1

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Jumaa 29 ga watan Mayun 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 8915.

An sallami mutum 2697 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 261.

A wani labarin daban, kunji cewa wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da wani yaro ke dambe da mahaifinsa a jihar Abia.

A cikin bidiyon, an hasko wani yaro mai suna Abuchi yana dambe da mahaifinsa a kofar gidansu a bainar jamaa.

An ji murya daga cikin bidiyon na yi wa yaron gargadi a lokacin da ya ke cigaba da dambe da mahaifinsa.

Wani da ke kallon abinda ke faruwa ya yi kokarin shiga tsakani domin ya raba fadan da ke tsakanin mahaifin da dansa.

Daga bisani ya tura matashin da mahaifinsa cikin gidansu.

A cewar rahotani, matashin yana fushi da mahaifinsa ne domin ya hana shi kudin cin abinci tun lokacin da aka kafa dokar kulle a jiharsu sakamakon bullar annobar coronavirus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel